logo

HAUSA

Sin: Ana Fatan Afghanistan Za Ta Kama Hanyar Raya Kasa Da Ta Dace Da Yanayinta

2021-09-10 14:38:52 CRI

Kwamitin sulhu na MDD ya yi babbar muhawara kan batun Afghanistan a jiya 9 ga wata, inda Geng Shuang, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD ya nuna cewa, yanzu kasar Afghanistan tana cikin wani muhimmin lokaci a tarihi. Kuma ana fatan za ta zabi hanyar raya kasa da ta dace da hakikanin halinta.

Geng Shuang ya kara da cewa, sanar da kafa gwamnatin wucin gadi da kungiyar Taliban ta Afghanistan ta yi, wani mataki ne da ya wajaba na mayar da tsari da oda a kasar da kuma sake gina kasar bayan yaki. Ya ce ana fatan kungiyar Taliban ta Afghanistan, za ta koyi darasi daga tarihi, ta cika alkawarinta, kuma ta hada kai da dukkan kabilu da rukunoni don kafa tsarin gwamnati mai kunshe da kowa, kana za ta aiwatar da matsakaitan manufofi a cikin gida da kuma waje, tare da kiyaye hakkokin mata da kananan yara, da tsayawa kan yaki da ‘yan ta’adda, da raya huldar abota da hadin gwiwa a tsakaninta da kasa da kasa, musamman ma kasashen da ke makwabtaka da ita. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan