logo

HAUSA

Babban jami’in Afghanistan: sabuwar gwamnati na maraba da zuwan masu zuba jari na kasar Sin

2021-09-08 16:42:09 CRI

Babban jami’in Afghanistan: sabuwar gwamnati na maraba da zuwan masu zuba jari na kasar Sin_fororder_微信图片_20210908160928

Ranar 7 ga wata bisa agogon wurin, Parwiz Karokhail, wakilin CGTN na kasar Sin ya zanta da Qari Yousuf Ahmadi, shugaban cibiyar watsa labarai na Taliban a birnin Kabul, hedkwatar mulkin kasar Afghanistan, inda Qari ya bayyana cewa, sabuwar gwamnatin kasarsa za ta kulla huldar kud-da-kud tare da Sin da Rasha da sauran kasashe, ba za ta kawo cikas ga yankin da take ciki da ma kasashen duniya ba. Haka kuma sabuwar gwamnatin tana maraba da zuwan daidaikun mutane da masana’antun kasar Sin don zuba jari da raya ayyukan kasuwanci a kasar Afghanistan, sa’an nan za ta samar musu muhallin zuba jari mai matukar tsaro. (Kande Gao)