Me ya sa Najeriya ba za ta zama Afghanistan ba?
2021-08-24 17:07:22 CMG
A kwanakin nan, halin da ake ciki a Afghanistan na janyo hankalin mutanen duniya. Da ma kasar Amurka na fatan ganin sojojin gwamnatin kasar Afghanistan su yi yaki da dakarun Taliban har tsawon watanni 3 kafin a bar Taliban shiga cikin Kabul, fadar mulkin kasar, amma Taliban sun samu nasarar takaita wannan wa’adi zuwa kwanaki 11, abun da ya ba duniya mamaki. A nasu bangaren, wasu kafofin watsa labaru na kasar Najeriya sun fara kwatanta yakin Afghanistan da yakin da gwamnatin kasar Najeriya take yi da Boko Haram, inda suka ce an kwashe kusan shekaru 20 ana fatattakar Boko Haram, amma har yanzu ba a kai ga kawar da kungiyar ba. Wai nan gaba kungiyar nan da wasu ke daukarta a matsayin “Taliban na Najeriya” ka iya kwaikwayon abun da ya faru a Afghanistan, ta sake tasowa har ma ta kwaci mulkin Najeriya.
Na fahimci yadda kafofin watsa labarun Najeriya suke damuwa kan yanayin tsaron kasar, da yadda suke neman jan hankalin gwamnatin kasar kan muhimmancin kawar da ta’addanci cikin sauri, amma duk da haka ina so in fadi wata maganar da za ta taimakawa kau da damuwa: Najeriya ba za ta zama Afghanistan ba, kana Boko Haram ba za ta samu damar kwatar mulki a Najeriya ba.
Ko da yake yadda sojojin gwamnatin kasar Najeriya ke yaki da mayakan Boko Haram, da yadda sojojin gwamnatin Afghanistan suka yi yaki da dakarun Taliban, duk yaki ne da aka yi tsakanin sojojin gwamnati da dakaru masu adawa da gwamnati, amma ainihin yanayin da suke ciki ya sha bamban. Yakin da ake yi a Najeriya shi ne domin yakar ta’addanci, yayin da yakin da ya abku a Afghanistan ya shafi kin harin sojojin kasashen waje, gami da kwatan mulki tsakanin kabilu daban daban.
Idan mun yi bincike kan dalilin da ya sa ake samun tashin hankali a Afghanistan, za mu ga cewa duk laifi ne na kasar Amurka. An kaddamar da Taliban a shekarar 1994, lokacin da aka fama da yakin basasa a Afghanistan, inda Taliban ta gabatar da ikirarinta na dakile jagoran yaki, da kafa gwamnati na Islama, don dawo da zaman sulhu, abun ya sa yake samun goyon baya daga wasu jama’a. Kana kungiyar na wakiltar moriyar ‘yan kabilar Pushtu, wadanda yawansu ya kai kashi 40% cikin daukacin al’ummar kasar. Wadannan dalilai sun sa Taliban ta girma cikin sauri, har ma ta kwaci mulkin kasar a shekarar 1996. Sai dai bayan da harin ranar 11 ga watan Satumban shekarar 2001 ya abku, kasar Amurka ta yi fushi kan yadda Taliban ke neman kare Usman Bin Laden, wanda ya kaddamar da harin a kasar, kana tana kwadayin matsayi mai muhimmanci da Afghanistan ta kasance a ciki a tsakiyar Asiya. Saboda haka, kasar Amurka ta tura sojoji Afghanstan, inda aka hambarar da gwamnatin da Taliban ta kafa, da maye gurbinta da bangarori masu adawa da Taliban. Amma wani abun da kasar Amurka ba ta yi tunani sosai a kansa ba shi ne, shin wata kasa kamar Afghanistan, wadda ta yi yaki da maharan Soviet Union har tsawon shekaru 10, kuma ta ci nasara a karshe, za ta iya hakuri da harin da wata kasa ta daban ta kai mata? Daga bisani, abun da ya faru ya zame wa kasar Amurka mafarki mai ban tsoro, inda dakarun Taliban suka kwashe shekaru 20 suna ta kokarin yaki da sojojin kasar Amurka, da sojojin gwamnatin Afghanistan, wadanda ke samun taimako daga kasar Amurka, da sanya Amurka kashe kudin aikin soja da ya kai dala triliyan 2.26, da asarar sojojinta 2300, har zuwa wani lokacin da kasar Amurka ta kasa ci gaba, sai ta yanke shawarar janye sojoji daga Afghanistan. Daga baya kasar Afghanistan ta koma yadda ta kasance shekaru 25 da suka wuce, lokacin da Taliban ta fara kama mulki a kasar, sai dai an samu asarar rayukan karin mutane fiye da dubu 100.
Yadda kasar Amurka ta ci tura a Afghanistan ya zama dole, domin da farko dai yadda ta kai hari ga kasar Afghanistan ya sa ba za ta samu sahihin goyon baya daga jama’ar Afghansitan ba. Na biyu, kamar yadda shugaba Joe Biden na kasar Amurka ya fada, aikin da kasar Amurka ta yi a Afghanistan “bai taba zama gina kasa ba”, don haka abun da ta haifar wa jama’ar Afghanistan yake-yake da rikice-rikice ne kadai, maimakon ci gaban al’umma. Na uku, tsarin dimokuradiya irin na kasashen yammacin duniya da kasar Amurka ta dora wa Afghanistan bai dace da yanayin kasar ba, lamarin da ya haddasa cin hanci da rashawa, da rarrabuwar kawunan al’umma. Na hudu, yadda kasar Amurka ke yawan amfani da jiragen sama marasa matuki wajen kai hare-hare daga sama ya haddasa hasarorin rayuka da jikkatar fararen hula da yawa, abun da ya fusata jama’ar Afghanistan matuka. Duk wadannan abubuwa sun tabbatar da cin tura da janyewar jikin sojojin Amurka daga kasar Afghanistan, sai dai jama’ar Afghanistan sun dade suna jira kafin wannan ranar ta zo.
Abun da ya faru a kasar Najeriya ya sha bamban da na Afghanistan sosai. Ko da yake Boko Haram ta yi ikirarin cewa za ta kafa daular Islama, amma hakika abubuwan da suka aikata ba su wuce kai hari ga kauyuka, da sace mutane don neman kudin fansa ba. Ba za su samu goyon baya daga jama’ar Najeriya ba, balle ma ta zama wata kungiyar da za ta gudanar da mulki. Yanzu kasar Najeriya na kokarin hadin gwiwa tare da kasashe makwabta, inda ake tara karin bayanai, da yin amfani da makaman zamani wajen yakar ‘yan ta’adda, tare da cimma nasarori da yawa, don haka tabbas ne za a samu kawar da Boko Haram a karshe.
A ganina,maimakon mai da hankali kan Boko Haram, ya fi dacewa gwamnatin Najeriya ta kara lura da aikace-aikacen karya dokoki ta hanyar nuna karfi. Domin da farko dai ana bukatar tabbatar da tsaro a wata kasa, kafin daga baya ta iya janyo jari, da samun damar raya masana’antu, da samar da guraben aikin yi, gami da kyautata zaman rayuwar jama’a, ta yadda tattalin arzikin kasar zai samu ci gaba sosai. Don cimma burin samun ci gaban Najeriya, dole ne a fara da kokarin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a kasar. (Bello Wang)