logo

HAUSA

MDD ta yi juyayin mutuwar shugaban kasar Chadi Deby

2021-05-04 16:14:44 CRI

MDD ta yi juyayin mutuwar shugaban kasar Chadi Deby_fororder_11

Babban taron MDD na ranar Litinin ya nuna juyayi game da mutuwar shugaban kasar Chadi Idriss Deby Itno.

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya jinjinawa marigayi shugaban Chadi, ya ce a madadin MDD, yana mika sakon ta’aziyya ga iyalinsa, da gwamnatin kasar da kuma al’ummar kasar ta Chadi.

Jami’in MDD ya ce, shugaba Deby ya yi aiki tukuru wajen tabbatar da zaman lafiyar kasarsa, da yankin tafkin Chadi, da ma nahiyar Afrika baki daya. Ya mayar da Chadi zuwa matsayin wata kasa mai karfin fada a ji bisa ga irin rawar da kasar ke takawa a shiyyar daga yankin Sahel har zuwa tafkin Chadi.

Ya kara da cewa, “karkashin jagorancinsa, a bisa abin da ni da kaina na shaida, Chadi ta bude kasarta ga dubban ‘yan gudun hijira daga makwabtan kasashe, inda ta tausaya musu wajen ba su mafaka da kuma taimaka musu gwargwadon karfinta.”

Guterres ya ce, Deby babban jigo ne a hadin gwiwa da MDD, musamman wajen yaki da ayyukan ta’addanci, da masu tsattsauran ra’ayi, da kungiyoyin masu aikata laifuffuka, ya ce wannan muhimmin lokaci ne ga kasar Chadi, don haka ya ba da tabbacin MDDr na yin aiki tukuru don cimma muradin al’ummar kasar Chadi da samun makoma mai kyau a nan gaba.(Ahmad)