logo

HAUSA

Shugaban kwamitin soja na wucin gadi ya yi kira ga jama’ar Chadi da su kara hada kai da ci gaba da dakile ta’addanci

2021-04-28 14:18:44 CRI

Shugaban kwamitin soja na wucin gadi Mahamat Idriss Deby Itno ya yi jawabi karon farko bayan rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasar, inda ya yi kira ga jama’ar kasar da su kara hada kansu don magance mawuyacin halin ake ciki, yana mai cewa kasar za ta ci gaba da dakile ta’addanci da sauke nauyin dake wuyanta na gudanar da harkokin kasa da kasa.

Cikin jawabin da ya gabatar jiya, Mahamat Idriss Deby Itno ya ce, saboda shugaban majalisar dokokin kasar ya yi watsi da ikonsa na ci gaba da rike mukaminsa ne ya sa aka kafa kwamitin mulkin soja na wucin gadi don magance matsalar da ake fuskanta yanzu, kuma burin kafuwarsa shi ne tabbatar da ikon mulkin kasar da tsaronta. A cewarsa, ana shirin muhawara tsakanin bangarori daban-daban dangane da kwamitin mulkin na lokacin wucin gadi, kuma za a shigar da duk wani aikin dake da alaka da moriyar kasa cikin shawarwarin, yana mai cewa, gwamnatin za ta sanar da hakikanin ajandar.

Ya ce, firaministan wucin gadi da kwamitin mulki na wucin gadi ya nada zai kafa wata gwamnati ta wucin gadi da za ta taimaka ga samun sulhu a kasar, kuma hukumar kafa dokoki ta wucin gadi da za a kafa, za ta tsai da sabun tsarin mulkin kasar, inda za a zabi mambobin kwamitin daga bangarorin wurare daban-daban. (Amina Xu)