logo

HAUSA

Shugaba Xi ya mika sakon ta’aziyya bisa rasuwar tsohon shugaban Chadi

2021-04-28 20:20:35 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya mika sakon ta’aziyyar rasuwar tsohon shugaban kasar Chadi Idriss Deby Itno, ga dan sa, kuma shugaban majalissar rikon kwarya ta sojojin kasar Mahamat Idriss Deby.

Cikin sakon nasa, shugaba Xi ya ce, a madadin gwamnati da al’ummar kasar Sin, da shi kan sa, yana taya gwamnatin Chadi matukar juyayin rasuwar tsohon shugaba Deby. Ya ce marigayin ya jagoranci al’ummar Chadi bisa burin kare ikon mulkin kasar da tsaron sassan ta, ya yayata manufofin ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’umma, ya kuma aiwatar da matakan wanzar da zaman lafiya da daidaito a yankin kasar.

Shugaban Xi ya ce a lokacin rayuwarsa, shugaba Deby ya dora muhimmancin gaske ga raya alakar kasar sa da Sin, ya inganta musaya da hadin gwiwa tsakanin sassan biyu a fannoni masu yawa. Kaza lika ya ba da muhimmiyar gudummawa, wajen bunkasa kawance da hadin gwiwar dake tsakanin Chadi da kasar Sin.  (Saminu)

Saminu