logo

HAUSA

Amurka Tana Kawo Barazana Ga Lafiyar Dukkan ‘Yan Adam

2021-08-14 20:13:37 CRI

Yawan mutanen kasar Amurka ya kai kaso 4 cikin dari bisa yawan al’ummun duniya, amma yawan wadanda ke kamuwa da cutar numfashi ta COVID-19 ya kai kaso 18 cikin dari bisa yawan masu fama da cutar a duk duniya. Wadannan alkaluma 2 sun nuna cewa, yadda Amurka ta gaza yaki da annobar ya kawo cikas wajen yaki da annobar a duniya. Amma da ganin yadda ake fama da matsaloli da dama wajen yaki da annobar a gida, gwamnatin Amurka ba ta dauki hakikanin matakai ba, ta bar annobar ta bazu zuwa sassa daban daban na duniya, lamarin da ya kawo barazana ga lafiyar al’ummun kasa da kasa.

Rahoton nazari da dandalin kwararru guda 3 na kasar Sin suka fitar cikin hadin gwiwa a kwanan baya, ya yi karin bayani kan yadda Amurka ta kau da kai daga yaduwar annobar a gida, ta kuma bar annobar ta bazu zuwa sassan duniya. Cikin sauki aka gano cewa, dalilin da ya sa yawan masu kamuwa da cutar COVID-19 ya wuce miliyan 200 a duk duniya yanzu haka, shi ne Amurka, wadda ta zama kasa ta farko a duniya ta fuskar baza annobar zuwa sassan duniya.

Sakamakon neman kiyaye ci gaban tattalin arziki da samun kuri’u, gwamnatin Amurka ta sanar da soke umurnin hana Amurkawa yin tafiye-tafiye a duniya a watan Agustan bara, lokacin da kasar ta fi fuskantar barazanar yaduwar annobar. Alkaluman da ofishin kula da harkokin yawon shakatawa na Amurka ya fitar sun nuna cewa, daga watan Afrilun shekarar 2020 zuwa watan Maris na bana, Amurkawa miliyan 23.195 ne suka tafi sassan duniya ta kasa da sama. Haka kuma daga watan Nuwamban shekarar 2020 zuwa watan Janairun shekarar 2021, lokaci ne da Amurka ta fara samun yawan masu kamuwa da cutar, matsakaicin yawan sabbin masu kamuwa da cutar ya kai dubu 186 a kowace rana. A daidai wannan lokaci ne kuma Amurkawa masu dimbin yawa suka tafi ketare, matsakaicin yawan Amurkawan da suka tafi ketare ya kai dubu 87 a kowace rana.

Sabili da haka ne ma annobar ta COVID-19 ta kara saurin yaduwa a sassa daban daban na duniya, lamarin da ya addabi al’ummun kasa da kasa. Kafofin yada labaru na kasashe da dama sun ruwaito cewa, 70% na masu kamuwa da cutar COVID-19 a Isra’ila, kwayar cutar da ta fito daga Amurka ce ta kama su, yayin da a cikin mutane 7000 da suka shiga Koriya ta Kudu tare da annobar, 30% sun fito daga Amurka, sa’an nan kuma a cikin masu kamuwa da annobar kusan 7000 a Australiya, 14% sun fito daga Amurka.

Shaidu sun nuna cewa, Amurka na da alhakin yaduwar annobar a sassan duniya. Don haka ta cancanci a binciketa dangane da asalin kwayar cutar ta COVID-19. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan