Zhao Lijian: Kasashe 55 sun mikawa WHO wasikar adawa da siyasantar da batun gano asalin cutar COVID-19
2021-07-20 19:49:27 CRI
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Zhao Lijian, ya ce kasashen duniya 55 sun mikawa babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, wasikar adawa da siyasantar da batun gano asalin cutar COVID-19.
Zhao Lijian ya ce, adadin kasashen dake adawa da mummunar manufar siyasantar da batun gano asalin cutar ya karu ne, saboda mafi yawan kasashen duniya na goyon bayan gaskiya da adalci, sabanin kasashe kalilan dake son mayar da batun siyasa, da murde gaskiya, da kalubalantar kimiyya.
Jami’in ya ce hakan ya kara tabbatar da burin sassan kasa da kasa, na rungumar gaskiya da adalci, da kuma bin doka yadda ya kamata.
Daga nan sai Zhao Lijian ya sake jaddada bukatar sassan da batun ya shafa, da su yi watsi da sanya siyasa cikin wannan lamari, ko dora alhaki kan wasu, su kuma dakatar da yiwa aikin zakulo asalin cutar da kasashen duniya ke yi kafar ungulu. Kaza lika ya yi kira ga masu aikin gwaje gwajen, da su gudanar da komai bisa kimiyya, da hadin gwiwar sassan kasa da kasa, ta yadda hakan zai ba da damar yakar annobar, da kare tsarin kiwon lafiyar bil Adama baki daya. (Saminu)
Labarai Masu Nasaba
- Sin za ta ci gaba da taka rawar gani a fannin yaki da annobar COVID-19
- IMF: Dabarun Kasar Sin Na Samun Ci Gaba Mai Inganci Za Su Taimaka Wajen Takaita Fitar Da Hayaki Mai Guba
- Tattalin arzikin yankin kudu da hamadar Sahara zai karu da kaso 3.4 a bana
- Guterres ya yi kira da a dauki matakai 6 don farfado da kasashe daga tasirin COVID-19