logo

HAUSA

IMF: Dabarun Kasar Sin Na Samun Ci Gaba Mai Inganci Za Su Taimaka Wajen Takaita Fitar Da Hayaki Mai Guba

2021-04-16 11:02:28 CRI

IMF: Dabarun Kasar Sin Na Samun Ci Gaba Mai Inganci Za Su Taimaka Wajen Takaita Fitar Da Hayaki Mai Guba_fororder_src=http___img.xmnn.cn_003_001_728_00300172803_ca5629cb&refer=http___img.xmnn

Babbar daraktar asusun ba da lamuni na duniya (IMF) Kristalina Georgieva, ta ce ci gaba da gyare-gyare da Sin ke yi da nufin samun ci gaba mai inganci da dorewa kuma bisa daidaito, ka iya taimakawa wajen takaita fitar da hayaki mai guba.

Kristalina Georgieva ta bayyana yayin taron karawa juna sani kan dabarar tunkarar yanayi da kiyayre muhalli cewa, matsawa daga zuba jari mai yawa, zuwa neman ci gaba ta hanyar amfani da kayayyaki da mara baya ga fadada hidimomi da bunkasa bangarorin fasahar zamani, za su rage bukatar makamashi da karuwar hayaki mai guba, lamarin da zai saukaka cimma muradun da ake da shi kan yanayi.

Da take bayyana haraji kan hayaki mai guda da ake fitarwa a matsayin dabara mafi inganci da arha wajen takaita fitar da hayaki mai guba, jami’ar ta ce harajin kwal na kasar Sin ka iya karuwa ta yadda zai magance fitar da hayaki mai guba.

Ta kuma bukaci kasashe da su dauki matsalar annobar COVID-19 a matsayin wata dama ta gina tattalin arziki mai jure yanayi da kuma dacewa da kare muhalli, wanda kuma zai taimaka wajen kai wa ga farfadowa mai dorewa. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha