logo

HAUSA

Wang Yi ya nuna adawa da ra’ayoyin Amurka da Japan na tsoma baki kan harkokin cikin gidan kasar Sin

2021-08-05 10:27:37 CRI

Wang Yi ya nuna adawa da ra’ayoyin Amurka da Japan na tsoma baki kan harkokin cikin gidan kasar Sin_fororder_wangyi

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya nuna adawa kan kalaman da kasashe kamar su Amurka da Japan suka yi kan batutuwan Xinjiang da Hong Kong na kasar Sin, tare da zargin kasar Sin bisa dalilan hakkin dan Adam

Wang ya bayyana haka ne, a yayin taron ministocin harkokin waje na kasashen gabashin Asiya karo na 11 da aka gudanar a daren jiya, inda ya gabatar da jawabi kan hadin gwiwar dake tsakanin kasashen gabashin Asiya ta kafar bidiyo. Wang Yi ya bukace su da su karyata wannan batu, tare da nuna kin amincewa.

Wang Yi ya bayyana cewa, harkokin Xinjiang da na Hong Kong, harkokin cikin gidan kasar Sin ne, kuma kalamai marasa dacewa irin wadannan, tamkar tsoma baki ne a harkokin cikin gida na kasar Sin ba tare da wata hujja ba, wadanda suka saba wa ka’idojin dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, da kuma ka’idojin kiyaye ikon mallaka cikin adalci na kasa da kasa.

Wang Yi ya ce, gwamnatin jihar Xinjiang ta gudanar da ayyuka a fili, da ba da amsa kan jita-jitar da aka gabatar ta hanyar gabatar da bayanai bisa shaidu, abin gaskiya da alkalumai. Jama’ar kananan kabilu ta jihar Xinjiang ciki har da ’yan kabilar Uygur, sun bayyanawa duniya hakikanin halin da suke ciki, don musunta jita-jitar da ake ta yadawa. Amma Amurka ba ta son saurara, har ma ta rufe idonta da gangan.

Wang Yi ya kara da cewa, tsara dokar tsaron kan yankin Hong Kong da yin kwaskwarima kan tsarin gudanar da zabe a yankin, sun taimaka wajen dawo da zaman lafiya a yankin, da kyautata dokokin yankin, da tabbatar da moriyar jama’ar yankin, da ma dukkan al’ummomin kasa da kasa dake yankin bisa doka, ta yadda hakan ya taimaka wajen tafiyar da manufar “Aiwatar da tsarukan mulki iri biyu a cikin kasa daya” a yankin yadda ya kamata. (Zainab Zhang)