logo

HAUSA

Wang Yi ya halarci taron ministocin harkokin wajen ASEAN da kasashen Sin da Japan da Korea ta kudu

2021-08-04 11:33:10 CRI

Wang Yi ya halarci taron ministocin harkokin wajen ASEAN da kasashen Sin da Japan da Korea ta kudu_fororder_962

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya halarci taron ministocin harkokin waje na kungiyar ASEAN da kasashen Sin da Japan da Korea ta kudu wato 10+3 ta bidiyo, da yammacin jiya Talata.

Wang Yi ya nuna cewa, kwayar cutar COVID-19 na sauya nau’inta sau da dama, kuma akwai bambancin farfadowar tattalin arziki tsakanin kasashe daban-daban, hakan ya sa ake fuskantar sabon kalubale a halin yanzu. Ya ce kamata ya yi a daga karfin kasashen gabashin Asiya na tinkarar kalubale da inganta karfi da kuzarin kasashen 10+3, ta yadda za a ba da tabbaci ga halin karko da wadata da yankin gabashin Asiya ya dade yana da su bayan iyakacin kokarin da suke yi. Ban da wannan kuma, kamata ya yi kasashen 10+3 su yi amfani da zarafi mai kyau na cika shekaru 25 da kafuwar hadin kan kasashen a badi, don tsai da shirin ayyukansu daga shekarar 2023 zuwa 2027, da taswirar da za a bi nan gaba don hidimar kungiya ta bai daya na yankin gabashin Asiya.

Ministocin kasashen sun jinjinawa ci gaban da kasashensu suka samu, kuma sun kai ga matsaya daya kan nazari da fitar da allurar rigakafin cutar COVID-19 cikin hadin kai da ingiza kafuwar cibiyar adana kayayyakin jiyya na ko ta kwana da baitulmalin ajiye abubuwa na ASEAN, kazalika, kasashen sun cimma matsaya daya kan nacewa ga manufar gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban-daban da gudanar da ciniki maras shinge da gaggauta amfani da RCEP tun da wuri, ta yadda za a karawa yankin kwarin gwiwa ta fuskar tattalin arziki. Ban da wannan kuma, sun jaddada wajibcin hadin kansu wajen habaka tattalin arziki na yanar gizo da tinkarar sauyin yanayi da dai sauransu don samun bunkasuwa da kiyaye muhalli tare.

Dadin dadawa, wakilan kasashen suna tuntubar juna mai zurfi kan wasu batutuwan shiyya-shiyya da bayyana kyakkyawar fata ga cimma nasarar gasar Olympics ta birnin Tokyo, tare da sa ran gasar Olmpics ta lokacin hunturu da za a gudanar a birnin Beijing a shekarar badi za ta cimma nasara. (Amina Xu)