logo

HAUSA

An gudanar da ayyuka daban daban a sassan kasar Sin domin tunawa da barkewar yakin kin harin Japan

2021-07-07 19:46:15 CRI

A yau Laraba ne ake cika shekaru 84, tun bayan harba bindigar Atilari a gadar Lugou, wadda ta alamta shirin kasar Sin na shiga yakin dakile harin Japanawa ‘yan mamaya.

Wannan yaki dai ya haifar da mummunar illa ga kasar Sin, a lokaci guda kuma ya zaburar da Sinawa wajen farkawa, da rungumar gwagwarmaya. A yau, domin tunawa da wannan rana, an fara gudanar da jerin ayyuka na tunawa da tarihin wannan yaki, tare da jinjinawa gudummawar ‘yan mazan jiya da suka sadaukar da rayukan su domin kare kasar Sin.   (Saminu)