logo

HAUSA

Kasar Sin ba ta cikin hadarin barkewar COVID-19

2021-08-13 20:52:53 CRI

He Qinghua, jami’i a hukumar lafiya ta kasar Sin, ya bayyana cewa, kasar Sin ba ta cikin hadarin barkewar COVID-19 a cikin kasar, yayin da kasar ta yi nasarar dakile bullar cutar ta baya-bayan nan tun a karshen watan Yuli.

He Qinghua wanda ya bayyana haka, yayin taron manema labaran da aka shirya Jumma’ar nan, ya bayyana cewa, ya zuwa jiya Alhamis, an ba da rahoton samun mutane 1,280 da suka kamu da cutar a cikin gida a birane 48 da ke larduna 18 a kasar. Daga cikin biranen, 36 sun ba da rahoton cewa, babu sabbin wadanda suka kamu da cutar, cikin kwanaki biyar a jere.(Ibrahim)

Ibrahim