logo

HAUSA

Sin ta yabawa kokarin mahukuntan Pakistan game da bincike da suke yi don gane da harin ta’addanci na Dasu

2021-08-13 11:28:50 CMG

Sin ta yabawa kokarin mahukuntan Pakistan game da bincike da suke yi don gane da harin ta’addanci na Dasu_fororder_4

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Hua Chunying, ta ce kasarta ta gamsu da kwazon mahukuntan Pakistan, na gudanar da bincike game da harin ta’addanci da ya auku a Dasu na kasar Pakistan.

Hua Chunying wadda ta yi tsokacin yayin taron manema labarai da ya gudana a jiya Alhamis, ta ce kawo yanzu, jami’ai a Pakistan na ci gaba da bincike kan aukuwar lamarin, kuma Sin da Pakistan din za su yi biyayya ga yarjejeniyar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, don zakulo dukkanin gaskiya, tare da tabbatar da an hukunta wadanda ke da hannu a cikin wannan aika aika.

Hua ta kara da cewa, ta’addanci abokin gabar daukacin bil adama ne, kuma Sin na matukar adawa da duk wani rukuni na amfani da ayyukan ta’addanci don cimma wata moriya. Kaza lika Sin na kira ga sassan kasa da kasa dake yankin ta, da su yi hadin gwiwa da juna wajen yaki da daukacin ‘yan ta’adda, tare da wanzar da moriyar bai daya, ta zaman lafiya da tsaro da ci gaban kasashen.  (Saminu)

Saminu