logo

HAUSA

An fara rajistar masu baje kolin CIIE karo na 5

2021-08-13 11:27:48 CMG

An fara rajistar masu baje kolin CIIE karo na 5_fororder_3

Mashirya bikin baje kolin hajojin da ake shigowa da su kasar Sin ko CIIE, sun ce an kaddamar da rajistar kamfanonin da za su halarci bikin karo na 5, wanda zai gudana tsakanin ranekun 5 zuwa 10 ga watan Nuwambar shekarar 2022.

Da yake tsokaci game da hakan, mataimakin darakta a ofishin shirya baje kolin na CIIE Liu Fuxue, ya ce ya zuwa yanzu, kamfanonin kasa da kasa sama da 20 ne suka tabbatar da cewa za su halarci bikin na shekarar 2022, wanda ake gudanarwa a birnin Shanghai na kasar Sin. Kuma a yayin baje kolin na 5, a karon farko, za a ware sashen musamman na baje kolin fasahohin kwaikwayon tunanin bil adama ko AI.

Jami’in ya kara da cewa, ya zuwa yanzu, an riga an nemi izinin amfani da fadin wuri da ya kai sakwaya mita 360,000, na yankin da aka tanada domin baje kolin karo na 4, wanda hakan ya yi daidai da adadin da ake fata.

Baje kolin CIIE, shi ne irin sa na farko a duniya, ya kuma haifar da manyan nasarori tun fara gudanar da shi karo 3 a jere. Za kuma a gudanar da karo na 4 ta yanar gizo daga birnin Shanghai, tsakanin ranekun 5 zuwa 10 ga watan Nuwambar dake tafe.  (Saminu)

Saminu