logo

HAUSA

An gano siffofin nau’in kwayar cutar SARS mai kama da Corona a shekarar 2008

2021-08-06 12:29:26 CMG

An gano siffofin nau’in kwayar cutar SARS mai kama da Corona a shekarar 2008_fororder_210806-faifai-5

Wata mukala da aka wallafa a 2008, a jaridar batutuwan kimiyya ta Amurka PNAS, ta bayyana kamalluwar nazarin fasali da siffofi da samar da nau’in kwayar cutar SARS mai kama da Corona.

Mukalar ta yi cikakken bayani kan dabarun fasali da siffofin dangin kwayar cutar SARS mai kama da Corona, ta kuma yi bayanin cewa, ba beraye ne kadai kwayar cutar za ta iya yiwa illa ba, har ma da sinadaran hanyoyin numfashi na jikin bil adama

Ralph Baric, farfesa a fannin nazarin yanayin yaduwar cututtuka a tsakanin jama’a, na Jami’ar North Carolina ne ya jagoranci rubuta mukalar.

A lokacin da aka wallafa wannan mukala, farfesa Barrick ya shadawa sauran abokan aikinsa cewa, yanzu suna da karfin tsarawa da fasalta dukkan nau’o’in kwayar cutar SARS kamar Corona. (Fa’iza Mustapha)

Fa'iza