logo

HAUSA

Sin Da Afirka Na Kokarin Raya Al’umma Mai Kyakkyawar Makoma Ga Dukkan ’Yan Adam Ta Fannin Kiwon Lafiya

2021-06-17 12:31:39 CRI

Sin Da Afirka Na Kokarin Raya Al’umma Mai Kyakkyawar Makoma Ga Dukkan ’Yan Adam Ta Fannin Kiwon Lafiya_fororder_sin2

A shekarar 2020, annobar cutar COVID-19 ta barke a sassa daban daban na duniya ba zato ba tsammani, ciki had da kasashen Afirka. A ranar 17 ga watan Yunin shekarar 2020, shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya jagoranci taron kolin musamman game da hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka, a fannin yaki da annobar tare da ba da jawabi, inda sassa daban daban suka yi musayar ra’ayoyi dangane da yaki da annobar a Afirka, da kara azama ga hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, da ma duk duniya baki daya wajen yaki da annobar, sun kuma cimma daidaito a wasu fannoni, lamarin da ya kara kuzari sosai wajen yaki da annobar a duniya.

Bayan shekara guda kuma, jama’ar Sin da Afirka sun ci gaba da mara wa juna baya, suna daidaita matsaloli tare, suna hada kansu wajen yaki da annobar ba tare da wata tsayawa ba. Don haka sun yi ta samun kyawawan sakamako, tare da karfafa gwiwar kasashen duniya, wajen yaki da annobar, da kuma ba da sabuwar gudummawa wajen raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan ’yan Adam ta fannin kiwon lafiya.

Yau shekara guda ke nan tun bayan da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar da muhimmin ra’ayi, a yayin taron kolin musamman na hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka wajen yaki da annobar COVID-19, wato tsayawa kan hada kan Sin da Afirka wajen yaki da annobar, da tsayawa kan kara azama wajen yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka, da tsayawa kan manufar cudanyar sassa daban daban, da tsayawa kan kyautata dankon zumunci a tsakanin Sin da Afirka, lamarin da ya nuna tsayayyiyar aniyar kasar Sin da kasashen Afirka, wajen yaki da annobar, da daidaita matsaloli cikin hadin gwiwa.

An kuma tsara manufar yin yaki da annobar da yin hadin gwiwar a-zo-a-gani a tsakanin Sin da Afirka, da fito da manyan tsare-tsare kan raya hulda a tsakanin bangarorin 2, da kara babban kuzari wajen ganin bayan annobar cikin hanzari, sakamakon hadin kan kasa da kasa.

Game da manufar taimakawa wadanda ke da matukar bukatar taimako, kasar Sin ta cika alkawarinta na taimakawa kasashen Afirka, wajen warware wasu matsaloli a zahiri, lamarin da ya nuna dankon zumunci a tsakanin bangarorin 2. A shekara guda da ta wuce, tawagar likitoci da kasar Sin ta tura zuwa wasu kasashen Afirka, sun shiga ayyukan yaki da annobar nan take bayan saukarsu a wurin.

Haka kuma tawagar kwararrun jami’an kiwon lafiya na kasar Sin, da tsarin hadin kan asibitocin Sin da Afirka da aka kafa cikin gaggawa, sun samar da kasashen Afirka kyawawan fasahohin yaki da annobar, dabaru da kayayyaki. Wasu kasashen Afirka sun kuma samu alluran rigakafin cutar COVID-19 kirar kasar Sin. Har ila yau, kasar Sin da wasu kasashen Afirka sun daddale ko cimma daidaito kan dakatar da biyan bashin da kasar Sin ke binsu, ta kuma soke wa kasashen Afirka da dama basussukan da ya kamata su biya a karshen shekarar 2020, karkashin taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka wato FOCAC.

Likitoci kan nuna tausayawa ga marasa lafiya. Likitocin kasar Sin da ke ba da tallafi a nahiyar Afirka ba su kula da tsaron lafiyarsu ba, sun ci gaba da ayyukansu a nahiyar, sun kuma sadaukar da kansu ba tare da son kai ba, sun mara wa asibitocin wurin kafa tsarin dakilewa, da kandagakin yaduwar annobar yadda ya kamata, a kokarin taimakawa jama’ar Afirka wajen kare kansu daga mummunar annobar.

Tun daga taron kolin musamman kan hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka, wajen yaki da annobar da aka gudanar a watan Yunin bara, har zuwa taron kolin lafiyar kasa da kasa a watan Mayun bana, ra’ayin da shugaba Xi Jinping ya gabatar dangane da raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan ’yan adam ta fannin kiwon lafiya ya dace da yadda ake yaki da annobar a kasashen Afirka, da ma duk duniya baki daya, ya kuma samu amincewa daga sassa daban daban na Afirka.

Cikin shekara guda da ta wuce, shugaba Xi Jinping ya tattauna da takwarorinsu na kasashen Afirka da dama ta wayar tarho, inda shugabannin Afirka suka amince da ra’ayin Xi Jinping a yayin taron kolin, sun kuma gode wa kasar Sin bisa goyon bayan da take bayarwa. Ban da haka kuma sun yi imanin cewa, kyawawan fasahohin kasar Sin na yaki da annobar, alluranta da maganinta, za su karfafa aniyar kasashen Afirka na samun nasarar yaki da annobar, za su kuma taka muhimmiyar rawa. Shugabannin kasashen Afirka sun nuna fatansu na kara hada kai da kasar Sin a fannonin yaki da annobar, da farfado da tattalin arziki, a kokarin samun sabon ci gaba wajen raya hulda a tsakanin Afirka da Sin da taron FOCAC. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan