logo

HAUSA

Wani masani ya yi gargadi game da illar da tattalin arzikin Afirka ta kudu zai fuskanta a nan gaba

2021-07-22 12:24:29 CMG

Wani masani ya yi gargadi game da illar da tattalin arzikin Afirka ta kudu zai fuskanta a nan gaba_fororder_ibrahim-5

Wani masani ya yi gargadin cewa, tattalin arzikin kasar Afirka ta kudu, zai fuskanci mummunan illa a shekarun dake tafe, bayan da aka yi kiyasin cewa, boren baya-bayan da ya barke ya kasar, ya haddasa asarar da ta kai Rand biliyan 50 na kudin kasar, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 2.9 kan GDPn kasar.

Wasu kungiyoyin tattalin arziki ma, suna hasashen bunkasar tattalin arzikin kasar a bana, za ta kai sama da kaso 3 cikin 100, bayan ya ragu da kaso 7 cikin 100 a shekarar da ta gabata, saboda rashin managartan matakan ci gaba, gami da matakan kullen COVID-19.

Kwamitin raya tattalin arziki da tsare-tsare mai suna eThekwini, ya bayyana cewa, bayan boren, kananan ‘yan tireda sama da 50,000 ne suka yi asarar hanyar da suke samun taro da sisi, inda aka yi kiyasin mutane miliyan 1.5 sun rasa hanyoyinsu na samun kudin shiga, baya ga wasu guraben ayyukan yi 150,000, dake fuskantar barazana.(Ibrahim)

Ibrahim