WHO: Adadin masu harbuwa da COVID-19 a Afirka ya karu da kaso 20% a gabar da cutar ke bazuwa a karo na uku
2021-06-18 12:53:50 cri
Hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, ta ce adadin masu harbuwa da cutar COVID-19 a nahiyar Afirka ya karu da kaso 20%, a gabar da cutar ke kara bazuwa a karo na uku.
Daraktar hukumar ta shiyyar Afirka Matshidiso Moeti ce ta bayyana hakan, cikin wata sanarwar da ofishin ta ya fitar, tana mai cewa Afirka na fuskantar zagaye na 3 na bazuwar COVID-19, a gabar da nahiyar ke fuskantar matsin a tsarin kiwon lafiya.
Moeti ta ce yanayin da ake ciki a yanzu, ya wajabta bukatar fadada matakan inganta tsarin kiwon lafiya, ciki har da samar da damar gwajin cutar, da killace masu dauke da ita, da jinyar su tare da gaggauta gano wadanda suka yi mu’amala da su.
Alkaluman WHO sun nuna cewa, adadin sabbin masu harbuwa da COVID-19 a Afirka sun karu zuwa sama da mutum 116,500 cikin mako guda, wato zuwa yammacin ranar 13 ga watan nan na Yuni, adadin da ya karu da mutum 91,000 kan na makon da ya gabaci hakan. Wanda hakan ke nuni ga karuwar masu harbuwa da cutar a wata guda.
Da wannan sakamako, adadin wadanda suka harbu da cutar a nahiyar ya karu zuwa sama da mutum miliyan biyar. Kaza lika Moeti ta ce cikin wannan adadi, kasashen Afirka 22 na dauke da kaso 20% na karuwar da aka samu cikin karshen makon jiya, yayin da adadin wadanda cutar ta hallaka ya karu da kaso 15 bisa dari a kasashen nahiyar 36 zuwa karshen makon na jiya. (Saminu)