logo

HAUSA

Kasar Sin ta shigo da busasshen barkono na farko daga Afirka

2021-08-05 10:16:15 CRI

Kasar Sin ta shigo da busasshen barkono na farko daga Afirka_fororder_a5c27d1ed21b0ef49e1153e5b5dab8d280cb3eb3

Hukumar kwastan dake birnin Changsha, babban birnin lardin Hunan ta sanar a jiya Laraba cewa, kasar Sin ta shigo da kilogiram 200 na busasshen barkono daga kasar Rwanda zuwa birnin na Changsha dake yankin tsakiyar kasar Sin.

A jiya ne dai hukumar kwastan dake Changshan ta ba da takardar shaida da killace rukunin barkonon da ta shigo da shi cikin yankin. Shugaban kamfanin GK International dake Hunan Yu Jian, kamfanin da ya jagoranci shigo da busasshen barkonon, za a sayar da shi ne ga dillalai, a kuma baiwa kwastomomi da kamfanonin dake sarrafa abinci a matsayin samfura.

Bisa tsarin kwangilar, masu samar da busassshen barkonon dake kasar Rwanda, za su rika fitar da tan 50,000 na busasshen barkonon zuwa lardin Hunan cikin shekaru biyar, za kuma a rika biyan su ne da kudin kasar Sin na RMB.

Bayanai na nuna cewa, kasar Sin ce ke kan gaba, wajen yawan masu amfani da busasshen barkono a duniya, inda ta fitar da tan 119,900 na busasshen barkano a watanni shida na farkon wannan shekara, adadin da ya karu da kaso 45.55 cikin 100 bisa na shekarar da ta gabata. Yayin da lardin Hunan ke zama kan gaba a fannin amfani da sarrafa busasshen barkono a fadin kasar.(Ibrahim)

Ibahim