logo

HAUSA

An cimma sabuwar yarjejeniya tsakanin Rwanda da Tanzania domin bunkasa ayyukan hadin gwiwa

2021-08-03 14:15:53 CRI

An cimma sabuwar yarjejeniya tsakanin Rwanda da Tanzania domin bunkasa ayyukan hadin gwiwa_fororder_tanzania-rwanda

Shugaban Rwanda Paul Kagame, ya ce yarjeniyoyin hadin gwiwa da aka rattabawa hannu tsakanin kasarsa da Tanzania a jiya Litinin, za su bayar da sabon kuzari ga aiwatar da ayyukan hadin gwiwa kamar na shimfida layin dogo.

Ya ce ba iyaka kadai ne ke tsakanin Rwanda da Tanzania ba, yana mai cewa, dangantaka mai karfi da burika na bai daya na kawo ci gaba ga jama’arsu, abu ne da ya kasance jigon hadin gwiwarsu. Paul Kagame ya bayyana haka ne ga wani taron manema labarai na hadin gwiwa da aka yi a birnin Kigali, tsakaninsa da takwararsa ta Tanzania Samia Suluhu Hassan dake ziyarar a kasar, jim kadan bayan rattaba hannu kan yarjeniyoyin hadin gwiwa 4 da suka shafi fannonin yada labarai da fasahar sadarwa da shige da fice da ilimi da sa ido kan kayayyakin da suka shafi kiwon lafiya.

A cewarsa, rattaba hannu kan yarjeniyoyin zai samar da sabon kuzari ga muhimman ayyukan more rayuwa da zuba jari na moriyar juna, musammam ma layin dogo da sana’ar samar da madara da ingantacciyar hanyar sufuri ta ruwa.

A nata bangaren, shugabar Tanzania Samia Hassan, cewa ta yi akwai abubuwa da dama da kasashen za su koya daga juna domin karfafa dangantakar cinikayya da tabbatar da ci gaba da raya tattalin arzikinsu da inganta rayuwar al’umma, tana mai cewa, rattaba hannu kan yarjeniyoyin zai bada dama ga cimma wadannan. (Fa’iza Mustapha)