Abincin 'yan saman jannati
2021-07-01 15:20:00 CRI
Abinci shi ne gaba da komai a rayuwar dan Adam. Yayin da ‘yan saman jannati ke shafe tsawon lokaci suna aiki a sararin samaniya, abinci shi ne abu mafi muhimmanci a gare su. Sakamakon ci gaban zamani, yanzu ‘yan saman jannati na iya cin abincin da siffarsu da dandanonsu ya yi kama da na duniyarmu.