logo

HAUSA

Shugaba Xi ya jajantawa takwaransa na Iraqi bisa gobarar da ta tashi a wani asibitin kasar

2021-04-27 20:47:15 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya mika sakon ta’aziyyarsa ga takwaransa na Iraqi Barham Salih, game da hadarin gobara da ya hallaka marasa lafiya da dama a wani asibiti dake kasar.

Shugaba Xi, ya ce a madadin gwamnatin Sin da daukacin al’ummar Sinawa, yana mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda gobarar ta rutsa da su, tare da wadanda suka jikkata a sanadiyyar hadarin.  (Saminu)

Saminu