logo

HAUSA

Gobara ta yi sanadin mutuwar mutane 41 a wani asibiti dake kudancin Iraqi

2021-07-13 10:39:00 CRI

Mutane a kalla 41 ne suka mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata, sanadiyyar wata gobara da ta tashi a wani asibitin kula da masu cutar COVID-19, dake lardin Dhi Qar na kudancin Iraqi.

Kamfanin dillancin labarai na kasar INA ya ruwaito cewa, gobarar ta tashi ne da yammacin jiya a cibiyar kebe wadanda suka kamu da cutar COVID-19 ta asibitin al-Hussein dake birnin al-Nasiriyah, mai nisan kilomita 375 daga kudancin Baghdad.

Ofishin yada labarai na firaministan Iraqi, Mustafa al-Kadhimi, ya sanar da cewa, firaministan ya kira wani taron gaggawa da ya kunshi wasu daga cikin ministoci da shugabannin tsaron kasar, domin tattaunawa kan gobarar da asarar da ta haifar.

A nasa bangare, shugaban majalisar dokokin Iraqi Mohammed al-Halbousi, ya wallafa a shafin tweeter cewa, za a tattauna batun yayin zaman majalisar na yau Talata. (Fa’iza Mustapha)