logo

HAUSA

Wakilin Sin a MDD ya yi kira da a tallafawa Iraqi

2021-02-17 15:48:58 CRI

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya yi kira ga sassan kasa da kasa da su tallafawa Iraqi, wajen shawo kan kalubalen siyasa da kasar ke fuskanta.

Geng wanda ya yi jan hankalin a jiya Talata, ya ce Iraqi na fuskantar matsalolin tsaro masu sarkakiya, da matsin tattalin arziki, da kuma yanayi na bukatar jin kai. Don haka ya kamata sassan kasa da kasa su samar da wani yanayi, wanda zai ba da damar warware matsalolin siyasar kasar, tare da kaiwa ga sulhu.

Jami’in ya ce, a bana batun gudanar da zabe, shi ne kan gaba a manyan ajandojin Iraqi. Kuma kasar Sin na fatan ganin zaben ya gudana lami lafiya, ta yadda zai gamsar da al’ummun kasar baki daya.

Kaza lika Geng Shuang, ya bukaci kasa da kasa da su tallafawa kokarin Iraqi, na cimma nasarar yaki da ayyukan ta’addanci, da samar da tsaron kasa, da kammala ayyukan kakkabe gyauron kungiyoyin ‘yan ta’adda, ciki har da na kasashen ketare, kamar kungiyar IS dake da sansanoni a cikin kasar.

Daga nan sai ya kara jan hankalin kasashen duniya, da su taimakawa Iraqin, a yakin da take yi da cutar numfashi ta COVID-19, da fannin bunkasa tattalin arzikin ta, tare da aiwatar da matakan kyautata rayuwar al’ummun kasar. (Saminu)