logo

HAUSA

Xi Jinping ya yi rangadi a Lhasa na Tibet

2021-07-23 16:15:28 CRI

Xi Jinping ya yi rangadi a Lhasa na Tibet_fororder_0723-Xi-Lasa-Faeza

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ziyarci yankin Lhasa na Tibet mai cin gashin kansa na kasar Sin da yammacin jiya Alhamis. Yayin rangadin, shugaban ya ziyarci wurin ibadar Drepung na addinin Budha da titin Barkhor da dandalin Potala, domin ganewa idonsa yadda harkokin addini ke gudana da yadda ake kare tsohon birnin da ma al’adun gargajiya na Tibet, tare kuma da gaisawa da jama’a. (Fa’iza Mustapha)