logo

HAUSA

Sin ta gudanar da taron kasa game da shirin tallafawa yankin Xinjiang

2021-07-22 11:26:01 CRI

Sin ta gudanar da taron kasa game da shirin tallafawa yankin Xinjiang_fororder_0722-Ahmad3.Xinjing

Wang Yang, babban jami’in jam’iyyar JKS, ya jaddada cikakkiyar aniyar gwamnati na samar da tallafin dogon zango ga yankin Xinjiang ta hanyar wani shirin tallafi na musamman na "pairing assistance" a yayin wani taron da aka gudanar tsakanin ranar Litinin zuwa Laraba.

Kasar Sin ta jima da aiwatar da shirin tallafin na "pairing assistance" a yankin Xinjiang, wanda aka fara shi tun a shekarar 1997, ya shafi samar da kudade, da kwarewa, da samar da tallafin ma’aikata daga fannoni daban daban ga yankin Xinjiang wadanda suka fito daga sauran shiyyoyin kasar.

Shirin tallafin na musamman ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen kawar da talauci da kyautata zaman rayuwar al’ummar Xinjiang da kara hada kan kananan kabilu, da kara bayyana alfanun dake tattare da shugabancin jam’iyyar JKS, da kuma karfafa tsarin gurguzu mai salon musamman na kasar Sin, a cewar Wang.

Wang ya kara da cewa, ya kamata a kara kokarin daga matsayin cudanyar al’adu tsakanin kabilu daban daban na yankin Xinjiang da sauran shiyyoyin kasar. (Ahmad)