logo

HAUSA

Xi Jinping Ya Gabatar Da Jawabi A Yayin Taron Koli Na JKS Da Jam’iyyun Siyasun Duniya daban daban

2021-07-07 11:16:50 CRI

Xi Jinping Ya Gabatar Da Jawabi A Yayin Taron Koli Na JKS Da Jam’iyyun Siyasun Duniya daban daban_fororder_01

Xi Jinping Ya Gabatar Da Jawabi A Yayin Taron Koli Na JKS Da Jam’iyyun Siyasun Duniya daban daban_fororder_02

Jiya Talata ne babban sakataren kwamitin tsakiyar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin JKS kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron koli na JKS da jam’iyyun siyasun kasa da kasa ta kafar bidiyo, tare da gabatar da jawabi, inda ya jaddada cewa, a matsayinta na muhimmin karfin kara azama kan ci gaban bil Adama, dole ne jam’iyya ta tsara manufa mai dacewa, ta kuma sauke nauyin faranta ran jama’a da kuma neman ci gaban dan Adam. Ya bayyana cewa, JKS tana son yin kokari tare da sauran jam’iyyun siyasun kasa da kasa wajen shimfida zaman lafiya a duniya, da ba da gudummowa ga ci gaban duniya da kiyaye tsarin dokokin kasa da kasa ba tare da kasala ba. A sanarwar bayan taron kolin na hadin gwiwa da aka fitar, ta bayyana burin bai daya na jam’iyyu mahalarta taron, na kiyaye zaman lafiya a duniya da kara kawo wa jama’a farin ciki.

Babban taken taron kolin shi ne “Kawo wa jama’a farin ciki: nauyi ne da aka dora wa jam’iyyu”. A cikin jawabinsa, Xi Jinping ya jaddada cewa, a halin yanzu, lokaci ya yi ne da ‘yan Adam za su sake zabi hanyar da za su bi. Jam’iyyu ciki da hadda JKS za mu yi zabi da kanmu, kuma an dora mana wannan nauyi dake wuyanmu. Xi ya ce, “Yayin da ake fuskantar kalubalolin bai daya, kowane mutum da kowace kasa ba za ta iya mayar da hankali kan moriyarta ta kadai ba tare da tunanin wasu ba. ‘Yan Adam ba za su samu mafita ba, sai sun hada kansu tare da zama tare cikin lumana. A matsayinta na muhimmin karfin kara azama kan ci gaban bil Adama, dole ne jam’iyya ta tsara manufa mai dacewa, ta sauke nauyin kawo wa jama’a farin ciki da kuma neman ci gaban dan Adam.”

Xi ya jaddada cewa, da farko dole ne jam’iyyu su ba da jagora wajen kokarin samun kyakkyawar makomar dan Adam ta bai daya. Na biyu, dole ne jam’iyyu su cimma daidaito tare da sauke nauyi tare, a kokarin tsayawa da yayata muradun bil Adama na bai daya wato neman samun zaman lafiya, ci gaba, adalci, demokuradiyya da ‘yancin kai. Na uku kuma, dole ne jam’iyyu su sauke nauyin kara azama kan ci gaba, a kokarin ganin al’ummun kasa da kasa, ta yadda za su kara jin dadi sakamakon ci gaba cikin adalci. Xi ya ce, “A yayin da ‘yan Adam suke neman samun farin ciki, bai kamata a manta da wata kasa ko wata kabila ba. Dukkan kasashe da kabilu da ke duniyarmu, kamata ya yi a ba su damar samun ci gaba da ‘yancin raya kansu cikin adalci.”

A cikin jawabinsa, Xi Jinping ya yi nuni da cewa, na hudu, dole ne jam’iyyu su inganta hadin gwiwarsu wajen tinkarar barazana da kalubale da ake fuskanta a duk duniya. Na biyar kuma, dole ne jam’iyyu su kyautata yadda ake tafiyar da harkoki, a kokarin inganta karfinsu na kawo wa jama’a farin ciki. Xi ya ce, “Hanyoyin samun farin ciki sun sha bamban da juna. Jama’ar kowace kasa su ne suke da iko na zabar hanyar raya kasarsu da salon tsarin mulkinsu. Wannan shi ne ma’anar kawo wa jama’a farin ciki. Har ila yau, al’ummun kasa da kasa, su ne suke da ikon bin tsarin demorakudiyyar da ya dace da su, wanda ba wasu tsirarrun kasashe suka tsara ba. amma akwai hanyoyi da dama na zabar tsarin demokuradiyya, ba hanya daya tilo ba. Al'ummar kasar ce, za su yanke hukunci game da ko dai kasarsu tana bin tsarin demokuradiyya ko a’a, ba wasu tsirarrun mutane ne ba.”

Xi Jinping ya yi nuni da cewa, JKS za ta ci gaba da sauke nauyinta yadda ya kamata, a kokarin ba da sabuwar gudummowa wajen kara kawo wa ‘yan Adam farin ciki. Kawar da talauci, buri ne na bai daya na al’ummun kasa da kasa, haka kuma muhimmiyar manufa ce da jam’iyyun kasa da kasa suke kokarin cimmawa. JKS na son kara fito da dabaru da karfinta na fitar da karin mutane daga talauci. Haka zalika, kasar Sin za ta yi iyakacin kokarin goyon bayan hadin gwiwar kasa da kasa kan yaki da annobar COVID-19, tare da kara ba da gudummowa wajen daidaita matsalar sauyin yanayi a duniya. JKS za ta nuna himma wajen kara azama kan kyautata tafiyar da harkokin kasa da kasa, a kokarin ganin ‘yan Adam sun daidaita kalubale tare kafada da kafada. Har ila yau, ka’idojin kasa da kasa, su ne ka’idoji da kasashen duniya suka amince da su, ba wasu tsirarrun mutane suka tsara ba. Wajibi ne a nuna adawa da matakan kashin kai da aka dauka da sunan manufar cudanyar sassa daban daban. Xi ya ce, “Kasar Sin, mamba ce a cikin gamayyar kasashe masu tasowa har abada. Za kuma ta tsaya tsayin daka kan kyautata wakilcin kasashe masu tasowa da kuma ikonsu na bayyana ra’ayi cikin tsarin tafiyar da harkokin kasa da kasa.”

A karshen jawabinsa, Xi Jinping ya sake nanata cewa, “JKS tana son ci gaba da hada kai da jam’iyyun siyasun duniya da kungiyoyin siyasu wajen kara azama kan ci gaban dan Adam, a kokarin kara ba da sabuwar gudummowa kan raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan dan Adam da samun duniya mai kyau da kowa zai ji dadin zama a cikinta.” (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan