logo

HAUSA

Hadin Gwiwar Sin Da Afrika Ya Karfafa Yaki Da Zazzabin Malaria

2021-07-03 16:14:15 CRI

Hadin Gwiwar Sin Da Afrika Ya Karfafa Yaki Da Zazzabin Malaria_fororder_src=http___5b0988e595225.cdn.sohucs.com_images_20180804_e12f15052605455a92b8ce9dd279c8c4.jpeg&refer=http___5b0988e595225.cdn.sohucs

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce kasashen Afrika za su iya kawo karshen zazzabin cizon sauro na malaria, zuwa shekarar 2030, bisa taimakon fasaha da Sin ta samar da nufin fatattakar cutar.

Shugaban shirin yaki da cututtukan yankuna masu zafi na ofishin hukumar WHO dake nahiyar Afrika, Akpala Kalu, ya ce muhimmiyar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen nahiyar ya bunkasa yakin da nahiyar ke yi da malaria.

A ranar Laraba ne WHO ta gabatar wa kasar Sin shaidar fatattakar cutar, a matsayin tukwicin nasarar da ta samu wajen yakin da ta shafe gomman shekaru tana yi da cutar.

A cewarsa, Afrika ta amfana daga shirin nan na 1-3-7 da Sin ta yi nasarar aiwatarwa. Ya ce tuni aka samu nasara a Tanzania bayan fara shirin, wanda ke jaddada muhimmancin bayar da rahoton barkewar cutar a rana ta farko da tabbatar ko an kamu bayan kwanaki 3 da kuma dakile yaduwarta a rana ta 7.

Ya ce kasar Sin ce ta taimakawa Tanzania aiwatar da wannan shiri na 1-3-7, daga shekarar 2016 zuwa 2018, wanda ya kai ga raguwar adadin masu kamuwa da cutar da kaso 80 a yankunan da ta fi tsanani.

Bugu da kari, ya ce za a aiwatar da shirin Sin na yaki da malaria a wasu kasashen Afrika 3, da suka hada da Burkina Faso da Senegal da Zambia. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha