logo

HAUSA

JKS Na Bin Wata Sabuwar Hanyar Raya Kasa Cikin Lumana

2021-07-03 20:46:20 CRI

JKS Na Bin Wata Sabuwar Hanyar Raya Kasa Cikin Lumana_fororder_jks

Xi Jinping, babban sakataren kwamitin tsakiyar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya bayyana wa kasashen duniya cewa, JKS na zura ido kan makomar bil’Adama, kuma tana hada hannu da dukkan sassan duniya da ke neman samun ci gaba. Ya ce har kullum kasar Sin na kokarin shimfida zaman lafiya a duniya da ba da gudummowa kan bunkasar duniya da kiyaye odar kasa da kasa.

Xi Jinping ya bayyana haka ne yayin babban taron murnar cika shekaru 100 da kafuwar jam’iyyar da aka gudanar a ranar 1 ga wata.

Al’ummar Sinawa sun dauki shekaru fiye da dubu 5 suna bin ruhun zaman lafiya, wanda kuma shi ne ruhun JKS. ‘Yan jam’iyyar daga zuriya zuwa zuriya suna ta gwagwarmaya wajen kiyaye zaman lafiya a duniya, daga jagorantar jama’ar Sin yaki da mahara Japanawa ‘yan Nazi, samun nasara a fagen yaki da ke gabashin duniya a babban yakin duniya na 2, tsayawa kan bin hanyar raya kasa cikin ruwan sanyi bayan kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin, tanadin “zaman lafiya” cikin kundin tsarin mulkin kasa da na jam’iyyar, da gabatar da tunanin raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan dan Adam da kara azama kan kafa hulda ta sabon salo a tsakanin kasa da kasa. Hakikanin abubuwan da ba za a iya musuntawa ba sun shaida cewa, jama’ar Sin ba su taba cin zalin mutanen kasashen waje ba, ba su taba muzgunawa mutanen kasashen waje ba, ba su taba bautar da mutanen kasashen waje ba. Ba sa yin hakan a yanzu, kuma ba za su yi ba a nan gaba ba.

Bisa abubuwan da suka faru a tarihinsu, kasashen yammacin duniya kan yi tsammanin cewa, dukkan kasashe masu karfi tabbas ne su yi danniya. Amma ba su fahimci tunanin JKS na tafiyar da mulkin kasa ba. Al’adun gargajiyar Sinawa, ruhun zaman lafiya na JKS da kuma yadda ake raya kasa bayan kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin, dukkansu sun nuna cewa, jam’iyyar mafi girma a duniya, wadda ke da mambobi fiye da miliyan 95, ba ta kawo barazana ga zaman lafiyar duniya ba, kuma tana dukufa wajen kiyaye zaman lafiya a duniya.

Jam’iyyar da ke mulkin kasar Sin tana bin ruhun zaman lafiya, amma hakan ba ya nufin za ta sadaukar da halaltattun muradunta, a’a, ko kusa ba ta yarda da a ci zalin jama’ar Sin, ko a muzguna musu, ko a bautar da su ba. Kamar yadda Xi Jinping ya fada a yayin babban taron murnar cika shekaru 100 da kafuwar JKS, duk wanda ke da irin wannan mugun nufi, tabbas zai girbi mummunan sakamako da ganin karfin zuciyar da jama’ar Sin fiye da biliyan 1.4 suke nunawa. Matsayin JKS ya nuna karfin zuciyarta da jan halinta da kuma kokarinta na kiyaye adalci da zaman lafiya a duniya. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan