logo

HAUSA

Tsohon jami’in Masar: JKS ce kashin bayan nasarorin kasar Sin

2021-07-02 15:37:29 CMG

Tsohon jami’in Masar: JKS ce kashin bayan nasarorin kasar Sin_fororder_faeza5

Tsohon Firaminsitan Masar, Essam Sharaf ya ce jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS) ce kashin bayan manyan nasarorin da kasar Sin ta samu.

Essam Sharaf ya bayyana haka ne yayin da yake tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Da yake tsokaci game da ‘ya’yan jam’iyyar da ya gana tare da aiki da su, yayin ziyarar da ya kawo kasar Sin sau da dama, ya bayyana su a matsayin jajirtattu kuma masu gaskiya dake da burin gina kasarsu.

Ya kara da cewa, “idan har ka hadu da ‘ya’yan jam’iyyar, to abu ne mai muhimmanci ka samu kwarin gwiwa daga dabarunsu, maimakon tattaunawa kan ayyukan hadin gwiwa kadai”. (Fa’iza Mustapha)

Faeza