logo

HAUSA

JKS Ba Ta Bukatar A Gaya Mata Abun Da Za Ta Yi

2021-07-03 16:46:22 CRI

JKS Ba Ta Bukatar A Gaya Mata Abun Da Za Ta Yi_fororder_sin

Xi Jinping, babban sakataren kwamitin tsakiyar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya bayyana wa kasashen duniya cewa, JKS da jama’ar Sin, za su ci gaba da bin hanyar da suka zaba da kansu tare da yin alfahari da ita, haka kuma za su tsai da kuduri kan makomar kasar da kansu. Xi Jinping ya bayyana haka ne yayin babban taron murnar cika shekaru 100 da kafuwar jam’iyyar da aka gudanar a ranar 1 ga wata.

Cikin shekaru 100 da suka gabata, bisa tunanin Marxism, JKS ta jagoranci daukacin al’ummar kasar wajen jure wahalhalu da daidaita matsaloli, tare da samun ‘yancin kanta da jama’arta, har ma kasar wadda ta taba fama da kangin talauci, ta zama ta biyu a duniya a fannin ci gaban tattalin arziki. Jama’ar Sin sun taba fama da matsalolin karancin abinci da tufafi, amma yanzu matsakaicin jimillar kudin shigar kowane mutum ya wuce dalar Amurka dubu 10. JKS da jama’ar Sin sun samar da abin al’ajabi a fannonin saurin ci gaban tattalin arziki da samun dawamammen kwanciyar hankali a zamantakewar al’ummar kasar, sun kuma kama wata hanyar gurguzu mai halin musamman na kasar Sin. Tarihi mai tsawon shekaru 100 ya shaida cewa, ba wanda zai iya ceton kasar Sin, sai tsarin gurguzanci kadai. Ba wanda zai iya raya kasar Sin, sai gurguzu mai halin musamman na kasar kadai.

A matsayinta na jam’iyya mafi girma da take mulkin kasa, hanyar raya kasa da jama’ar Sin suka zaba karkashin shugabancin JKS, ta kara kuzari kan ci gaban duniya. A shekaru da dama da suka wuce, gudummawar kasar Sin ga bunkasar tattalin arzikin duniya ta kai kaso 30 cikin 100. An yi kiyasin cewa, shawarar “Ziri daya da hanya daya” da aka aiwatarwa za ta fitar da mutane miliyan 7 da dubu 600 daga kangin talauci a kasashen da suka shiga shirin, yayin da tuni wasu miliyan 32 suka fita daga talauci. Sa’an nan kuma, kasar Sin ta aiwatar da yarjejeniyar Paris dangane da sauyin yanayi, inda ta sanar da manufar tabbatar da yawan hayaki mai dumama yanayin duniya da za ta fitar zai kai matsayin koli kafin shekarar 2030 da kuma kokarin samun daidaito tsakanin yawan hayakin da za ta fitar, da yawan abubuwan da za su shawo kan hayakin kafin shekarar 2060. Ci gaban kasar Sin ya kara azama kan ci gaban kasashen duniya baki daya.

Haka zalika hanyar da kasar Sin ke bi wajen samun ci gaba ta samar da sabbin hanyoyi a fannin raya zamantakewar al’ummar na zamani. A baya wasu kasashe masu tasowa su kan yi koyi da kasashen yammancin duniya don samun dabarar raya kasa ta zamani. Amma hanyoyin da kasashen yammacin duniya suke bi ba su dace da su ba. Hanyar kasar Sin ta shaida cewa, raya kasa ta zamani ba ya nufin raya kasa ta hanyar da kasashen yammacin duniya suke bi. Ya zama tilas a bi hanyar da ta dace da kowace kasa don tabbatar da ci gaba irin na zamani.

Hakikanin abubuwa da lokuta dukkansu sun shaida cewa, hanyar gurguzu mai halin musamman na kasar Sin ta dace da kasar sosai, kuma tabbas za ta kara samar wa kasar Sin da ma duniya kyakkyawar makoma. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan