logo

HAUSA

Shawarwarin Kasar Sin Sun Bayyana Yadda Sin Da Afirka Suke Tsayawa Juna A Lokacin Farin Ciki Da Akasinsa

2021-05-26 14:11:29 CRI

Shawarwarin Kasar Sin Sun Bayyana Yadda Sin Da Afirka Suke Tsayawa Juna A Lokacin Farin Ciki Da Akasinsa_fororder_sin

Kwanan baya, an gudanar da taron kolin tattara kudi na kasashen Afirka da taron manyan jami’an MDD kan wanzar da zaman lafiya da tsaro na daya bayan daya, inda kasar Sin ta yi kira da a goyi bayan kasashen Afirka dangane da yaki da annobar COVID-19 da tabbatar da tsaro, tare da gabatar da wasu shawarwari. Shawarwarin da kasar Sin ta gabatar, sun shaida yadda kasar Sin take nuna wa kasashen Afirka aminci da sahihanci da gaskiya, sun kuma bayyana yadda kasar Sin da kasashen Afirka suke tsayawa juna a lokacin farin ciki da akasinsa.

A halin yanzu wasu kasashen Afirka suna fuskantar kalubale mai sarkakiyya wajen samun zaman lafiya da tsaro a cikin gida, yayin da yaduwar annobar COVID-19 ta rura wutar rashin kwanciyar hankali a yankin. Ban da haka kuma, yadda wasu kasashe masu sukuni suke kare muradun kasa fiye da batun riga kafin COVID-19 da yadda suke kokarin boye rigakafin, ya haddasa karancin rigakafi a nahiyar Afirka. Alkaluman MDD sun nuna cewa, a cikin alluran rigakafin miliyan 140 da aka yi wa al’ummar kasa da kasa, miliyan 24 ne kawai aka yi wa al’ummar kasashen Afirka. Yawan mutanen da aka yi musu alluran bai kai kashi 1.5 cikin kashi 100 ba a Afirka.

Kasar Sin ta gabatar da shawarwari da dama, a kokarin taimaka wa kasashen Afirka warware matsalolin da suke addabar su sosai. A yayin taron koli kan tattara kudi na kasashen Afirka, kasar Sin ta gabatar da shawarwari guda 4, wato sassauta matsin lambar da kasashen Afirka suke fuskanta ta fuskar bashi, kara azama kan farfado da tattalin arzikin duniya, sa kaimi kan sauya hanyar raya tattalin arzikin Afirka, da tabbatar da raba alluran rigakafin COVID-19 a kasashen Afirka cikin adalci. Haka kuma, a yayin taron manyan jami’an MDD kan samun zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afirka, wanda kasar Sin ta kira, ta ba da nata shawarwari a fannoni guda 4, wato taimakawa kasashen Afirka kau da tasirin yaki da annoba, daidaita batutuwan da suka shafi wanzar da zaman lafiya a Afirka, rage bambancin dake tsakanin Afirka da sauran sassan duniya ta fuskar bunkasuwa, da maido da adalci a fannin tafiyar da harkokin kasa. Har ila yau, yayin da kasar Sin da kasashen Afirka suke dakile da kandagarkin annobar ta COVID-19, sun gabatar da shawarar abota ta goyon bayan bunkasuwar Afirka, inda suka yi kira ga kasashen duniya da su kara karfinsu na mara wa kasashen Afirka baya a fannonin yaki da annobar, sake gina kasa bayan annobar, zuba jari da yin ciniki, da sassauta da rage basussukan da ake bin kasashen Afirka.

Jerin shawarwarin da kasar Sin ta gabatar, sun biya hakikanin bukatun kasashen Afirka, sun kuma kasance kyawawan hanyoyi a fannin karfafa gwiwar kasashen duniya su taimaka wa kasashen Afirka daidaita kalubalen da suke fuskanta. Wasu al’ummun kasashen Afirka sun yaba da shawarwarin kasar Sin sosai. A ganinsu, kasar Sin ta sauke nauyin dake bisa wuyanta, tare da ba da muhimmanci kan huldar dake tsakaninta da kasashen Afirka. Lamarin da ya nuna aniyar kasar Sin ta ci gaba da himmantuwa wajen taimakawa Afirka fita daga mawuyancin hali.

Hakika dai, ba shawarwari kawai ba, kasar Sin ta dauki matakan a-zo-a-gani wajen tallafawa Afirka. Har kullum ta kan cika alkawarin da ta yi wa abokanta na Afirka a fannonin mara musu baya wajen yaki da annobar, rage basussukan da take binsu, kiyaye zaman lafiya da dai sauransu. Alkaluma sun nuna cewa, tawagar ma’aikatan lafiya guda 46 da kasar Sin ta tura kasashen Afirka sun shiga aikin yaki da annobar a wurin nan da nan. Kungiyoyin kwararru masu ilmin likitanci guda 15 da suke zagaya kasashen Afirka da kuma tsare-tsare guda 43 da aka kafa cikin gaggawa na hadin kan asibitocin kasashen Sin da Afirka, sun samar wa kasashen Afirka kyawawan fasahohi da dabaru da kayayyaki. Ya zuwa yanzu kasar Sin ta riga ta samar wa kasashen Afirka fiye da 30 ko tana shirya samar musu rigakafin. Kasar Sin ta daddale yarjejeniyar dakatar da biyan bashi ko cimma daidaito kan dakatar da biyan bashi tare da kasashen Afirka 16, don aiwatar da shawarar kungiyar G20. Ta kuma soke basussukan da take bin kasashen Afirka 15 karkashin taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC, wadanda ya kamata su biya a karshen shekarar 2020. Ya zuwa yanzu kasar Sin ta tura jirgin ruwan soja sau 37 domin ba da kariya a mashigin tekun Aden, yayin da sojojin kasar Sin masu kiyaye zaman lafiya 2043 suke gudanar da aikinsu a nahiyar Afirka.

Kasar Sin na darajanta dankon zumuncin da ke tsakaninta da kasashen Afirka. Duk da sauye-sauyen da ake fuskanta a kasashen duniya, kasar Sin ba ta sauya aniyarta ta inganta hadin kanta da kasashen Afirka ba. Shaidu sun nuna cewa, har kullum kasar Sin na tsayawa kan goyon bayan kasashen Afirka yaki da annobar COVID-19, tana kuma shiga ayyukan raya da farfado da Afirka, da goyon bayan kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a Afirka. Kasar Sin da kasashen Afirka suna kara raya makomarsu ta bai daya. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan