logo

HAUSA

Batun cin bashi a kasashen Afirka da alakarsa da kasar Sin

2021-05-31 13:46:22 CMG

Batun cin bashi a kasashen Afirka da alakarsa da kasar Sin_fororder_bello-0531

Tun bayan barkewar annobar COVID-19, al’ummun duniya na kara mai da hankali kan wani yanayin da wasu kasashen dake nahiyar Afirka suke ciki na yawan cin bashi. Sai dai wasu kasashen yammacin duniya na yada jita-jitar cewa, bashin da kasar Sin ta samarwa kasashen Afirka ya sa su fadawa cikin tarko.

Hakika a wasu bukukuwan da suka gudana a watannin baya, wadanda suka hada taron koli na kungiyar G20, da babban taron aikin lafiya na duniya, da taron tattara kudi don raya tattalin arzikin kasashen Afirka, da dai sauransu, an tattauna batun yafe wa kasashen Afirka basusukan da ake binsu. A sa’i daya, an fara gano dalilin da ya sa ake samun matsalar cin bashi a nahiyar Afirka.

Basusukan dake kan kasashen Afirka na ta karuwa, bayan rikicin hada-hadar kudi da ya shafi kasashe daban daban a shekarar 2008. Kana yanayin batun ya kara tsananta bayan barkewar annobar COVID-19, inda a shekarar 2020, yawan kasashen dake nahiyar Afirka wadanda suke fuskantar hadarin samun matsalar bashi ya kai 20.

A cewar wasu kwararrun masana ilimin tattalin arziki, dalilin da ya sa ake samun wannan matsala a wasu kasashen Afirka, shi ne domin da ma tsarin tattalin arzikin kasashen ba shi da karfi, kana wasu kungiyoyi masu zaman kansu na bayar da dimbin basusuka ga kasashen. Ban da wannan kuma, karuwar kudin ruwan da ake bayarwa a bankunan kasar Amurka, da mummunan tasirin annobar COVID-19 kan tattalin arziki, dukkansu sun tsananta matsalar cin bashi a Afirka.

Sai dai don daidaita matsalar bashi, ko za a iya soke bashin da ake bin kasashen Afirka kawai? Dangane da batun, shugaban bankin raya yammacin Afirka Serge Ekue ya ce, maimakon soke bashi, ya fi kyau a kara samar da bashi, wanda wa’adinsa ya wuce shekaru 7, kana yawan kudin ruwansa ya kasance kashi 3% maimakon 6%. Domin hakan zai taimakawa farfado da tattalin arzikin kasashen Afirka.

Game da basusukan da kasar Sin ta baiwa kasashen Afirka, wasu kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya sun saba da kokarin nemo laifi daga cikinsu. Kana su kan gyara alkaluman bashi don kambama lamarin. Sai dai bisa alkaluman da bankin duniya ya samar, cikin yawan basusukan da darajarsu ta kai dala biliyan 625 da ake bin kasashen Afirka wadanda suke kudu da hamadar Sahara, kawo karshen shekarar 2019, bashin da aka samu daga kasar Sin bai kai kashi 20% ba.

A cewar mujallar Jeune Afrique ta kasar Faransa, wasu manyan kamfanoni na kasa da kasa ne suka kasance wadanda suka fi samar da bashi ga kasashen Afirka, kamfanonin da suka hada da masu sarrafa kadarori, da asusun ba da fensho ga tsoffi, da bankuna masu zaman kansu, da kamfanonin inshora, da dai makamantansu. Kana yawan bashin da suka samar ya kai kashi 40% cikin daukacin basusukan da ke kan kasashen Afirka. Sa’an nan asusun ba da lamuni na duniya IMF, da bankin duniya sun samar da bashin da ya kai kashi 25% na basusukan da kasashen Afirka suka ci. A nasa bangare kulob din Paris, shi ma ya samar da dimbin rance ga kasashen dake nahiyar Afirka.

Wadannan alkaluman sun shaida cewa, yawan basusukan da kasashen Afirka suke ci daga kasar Sin, bai kai wani matsayin da zai sa kasashen Afirka “fadawa cikin tarko” ba.

Duk da haka, wasu kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya na kokarin yada jita-jita, cewa wai kasar Sin na neman kwatar albarkatu da kadarori na kasashen Afirka, lokacin da suka kasa biyan bashi. Zancen da shugabannin Kenya, da Rwanda, da Angola, da Zambia da dai sauransu dukkansu suka karyata.

A cewar Ibrahima Fofana, firaministan kasar Guinea, yadda wasu kasashen yammacin duniya suke dora laifi ga kasar Sin, na da nufin bata huldar hadin gwiwa dake tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin. Ya ce, kudin da kasashen Turai suke zubawa nahiyar Afirka na ta raguwa, tun daga shekarun 1990. Sabanin yadda mutanen nahiyar Turai suke nisanta kansu da Afirka, Sinawa sun shiga nahiyar Afirka tare da dimbin jari, da tsarin hadin gwiwa mai kima na dogon lokaci. (Bello Wang)

Bello