logo

HAUSA

Yang Jiechi zai halarci taron manyan jami'an BRICS karo na 10 kan batutuwan tsaro

2020-09-16 19:48:30 cri

A gobe Alhamis ne, mamban hukumar siyasa ta kwamitin koli na JKS, Yang Jiechi zai halarci taron manyan wakilan BRICS karo na 10 kan batutuwan da suka shafi tsaro.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Wang Wenbin, wanda ya bayyana haka yayin taron manema labarai da aka shirya, ya bayyana cewa, Yang, wanda har ila shi ne, darektan ofishin hukumar kula da harkokin waje ta kwamitin koli na JKS, zai halarci taron da zai gudana ta kafar bidiyo ne, bisa gayyatar sakataren hukumar tsaron kasar Rasha, Nikolai Patrushev. (Ibrahim)