logo

HAUSA

Yang Jiechi ya tattauna da sakataren wajen Amurka ta wayar tarho

2020-03-17 19:19:46 cri

A jiya ne, mamban hukumar siyasa na kwamitin koli na JKS, Yang Jiechi, ya tattauna ta wayar tarho da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo bisa gayyatar da ya yi masa, inda ya bayyana cewa, yanzu abu mafi muhimmanci shi ne, kasashen duniya su hada karfi da karfe wajen yaki da COVID-19.

Jami'in na kasar Sin ya ce, wasu 'yan siyasar Amurka sun sha sukar kasar Sin da ma matakan da take dauka na yaki da wannan annoba da kokarin mayar da kasar saniyar ware, matakin da ya shafi al'ummar Sinawa.

Don haka, ya bukaci bangaren Amurka, da ya hanzarta gyara halayensa marasa kyau da kuma daina zargin kasar Sin ba tare da kwararan hujjoji ba.

Bugu da kari, kasar Sin ta bukaci kasar Amurka, da ta yi la'akari da muradu da kudurin al'ummomin dake kasashen biyu da ma sassan duniya baki daya, ta karfafa tattaunawa da hadin gwiwa da kasar Sin da ma kasashen duniya, kana ta hada hannu a kokarin da ake na kare lafiyar al'ummar duniya baki daya. (Ibrahim)