logo

HAUSA

Yang Jiechi Ya Bayyana Matsayin Kasar Sin A Bayanin Fara Tattaunawar Manyan Jami’an Sin da Amurka Bisa Manyan Tsare-tsare

2021-03-19 14:58:20 CRI

Yang Jiechi Ya Bayyana Matsayin Kasar Sin A Bayanin Fara Tattaunawar Manyan Jami’an Sin da Amurka Bisa Manyan Tsare-tsare_fororder_0319-1

Ranar 18 ga wata, Yang Jiechi, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya ta Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin kuma darektan ofishin kula da harkokin waje na kwamitin tsakiyar JKS, da Wang Yi, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar sun halarci taron tattaunawar manyan jami’an Sin da Amurka bisa manyan tsare-tsare tare da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken da Jake Sullivan, mai ba da shawara ga shugaban Amurka dangane da harkokin tsaro.

Bayan da bangaren Amurka ya bayyana bayanin fara tattaunawar, Yang Jiechi ya yi jawabi, inda ya jaddada cewa, kasar Sin tana gudanar da tattaunawar a Anchorage ne bisa gayyatar Amurka. Jama’ar kasashen 2 da kasashen duniya suna sa ran samun sakamakon a-zo-a-gani a yayin tattaunawar.

Yang Jiechi ya kara da cewa, kasar Sin na fatan za a yi tattaunawar cikin sahihanci ba tare da wata rufa-rufa ba. Kasashen Sin da Amurka, manyan kasashe ne a duniya, kuma suna sauke nauyin dake wuyansu a yankuna da ma duniya baki daya a harkokin zaman lafiya, kwanciyar hankali, da ci gaba.

Yang ya nuna cewa, kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan kiyaye moriyar bai daya ta bil Adama wato zaman lafiya, ci gaba, adalci, dimokuradiyya, da ‘yancin kai. Tana nacewa kan kiyaye tsarin kasashen duniya, inda aka mayar da MDD a matsayin cibiyar tsarin, tare da mayar da dokokin kasa da kasa a matsayin tushen odar kasa da kasa, a maimakon wani tsarin da wasu kasashe kalilan suka tsara. Yawancin kasashen duniya ba su kallon duniya kamar yadda Amurka take kallonta, kana ba su amince da cewa, za a iya wakiltar ra’ayoyin kasashen duniya da ra’ayi na kasar Amurka ba, kuma ba su amince da ka’idojin da wasu kasashe kalilan suka tsara a matsayin ka’idojin kasa da kasa ba. Amurka tana bin dimokuradiyya irin nata, yayin da kasar Sin take bin irin nata. Kasar Sin tana bin hanyar raya kasa cikin lumana, kana tana namijin kokarin wanzar da zaman lafiya da ci gaba a yankuna da ma duniya baki daya, tare da kiyaye kundin tsarin MDD da ka’idojin majalisar, a maimakon yin amfani da karfin soja da ta da kura a duniya, kamar yadda Amurka take yi. Amurka tana fuskantar matsaloli daban daban a fannin kiyaye hakkin dan Adam. Kamata ya yi Amurka ta sauya siffarta, da kula da harkokinta, a maimakon dora wa kasashen duniya laifi kafin ta daidaita batutuwanta yadda ya kamata. Bai kamata ta soki kasar Sin dangane da hakkin dan Adam da dimokuradiyya ba. Yadda jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin take jagorantar kasar Sin da tsarin siyasar kasar Sin sun samu goyon baya daga jama’ar Sin cikin sahihanci. Duk wani yunkurin neman sauya tsarin zamantakewar al’ummar kasar Sin ba zai ci nasara ba.

Yang Jiechi ya yi fatan cewa, Amurka za ta yi watsi da tunanin cin moriya da faduwar wani, da dakatar da daidaita harkokin kasa da kasa bisa dokokinta na gida. Ta kuma dakatar da kawo illa ga cinikin da ke tsakanin Sin da Amurka bisa hujjar tsaron kasa. Taiwan, Hong Kong da Xinjiang, yankunan kasar Sin ne da ba za a iya raba su da Sin ba. Kasar Sin bata amince Amurka ta tsoma baki cikin harkokin cikin gidanta ba. Za ta kuma ci gaba da mayar da martani. Ba wanda ya baiwa Amurka iznin ba da umurni ga kasar Sin ba, kana jama’ar Sin ba su yarda da haka ba. Kasar Sin tana mu’amala da sauran kasashe ne bisa ka’idar girmama juna. Tarihi ya shaida cewa, idan ana matsawa kasar Sin lamba, to, moriyar kai za a illata.

Yang Jiechi ya ci gaba da cewa, ana samun manyan sauye-sauye a duniya a halin yanzu. Ya zama tilas kasashen 2 su kara tuntubar juna a sabon halin da ake ciki, da daidaita sabani yadda ya kamata, da kara azama kan yin hadin gwiwa a tsakaninsu. Hakikanan abubuwa sun nuna cewa, adawa da juna ba zai amfana wa Amurka ba. Kamar yadda shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya fada, dole ne Sin da Amurka su rungumi akidun kaucewa rikici, da fito na fito, tare da martaba juna da cimma gajiya tare. Kana a cewar shugaba Joe Biden na Amurka, Sin da Amurka su kaucewa rikici, da fito na fito. Don haka ya kamata kasashen 2 su aiwatar da ra’ayi daya da shugabannin kasashen 2 suka cimma a tsanake, da maido da huldar da ke tsakaninsu kan hanyar samun ci gaba yadda ya kamata. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan