logo

HAUSA

Tashar ciniki marar shinge ta Hainan ta cika shekaru uku da kafuwa

2021-04-13 13:50:03 CRI

A yau ne tashar ciniki marar shinge ta Hainan ta cika shekaru uku da kafuwa. A cikin shekaru uku da suka gabata, an fitar da “shirin gina tashar ciniki marar shinge ta Hainan” tare da aiwatar da shi, kuma jerin manufofi masu gatanci sun jawo dimbin kamfanoni masu jarin waje.

A Hainan, akwai yanki na gwajin harkokin shakatawa don kiwon lafiya mai suna yankin Lecheng na gwajin harkokin shakatawa don kiwon lafiya ta kasa da kasa, wanda ya kasance irinsa na farko. A yankin, masu fama da rashin lafiya suna iya samun aikin jinya mafi inganci ba tare da sun fita zuwa wata kasar waje ba. Bisa namijin kokarin da aka shafe shekaru da dama ana yi, yanzu haka yankin ya samu ci gaba ta fannin jinyar masu fama da ciwon sankara da ma samar da hidimomin jinya ta sauran fannoni, wanda kuma ya taimaka ga hada albarkatun jiyya masu ci gaba na duniya da bukatun gida. Dr. Michael Tierney, shehun malami a cibiyar nazarin harkokin likitanci ta Nebraska ta Amurka ya ce,“Muna son yin amfani da manufofi masu kyau da ake aiwatarwa a yankin Lecheng na gwajin harkokin yawon shakatawa don kiwon lafiya da ke Bo’ao, mun yi nazari kan har hada sabbin magunguna bisa ga nazarin da kasashen Sin da Amurka suka gudanar, kuma muna da imanin cewa, hadin karfin kasashen biyu zai samar da karin nasarori.”

Tashar ciniki marar shinge ta Hainan ta cika shekaru uku da kafuwa_fororder_微信图片_20210413161008

Alkaluman da aka samar sun yi nuni da cewa, a shekarar 2020, yankin Lecheng na gwajin harkokin yawon shakatawa don kiwon lafiya da ke Bo’ao ya karbi masu yawon shakatawa don kiwon lafiya da suka kai dubu 83.9, adadin da ya karu da kaso 11.87% bisa na makamancin lokacin bara. Baya ga haka, ya zuwa yanzu, yankin ya kulla huldar hadin gwiwa da kaso 80% na fitattun kamfanonin samar da magunguna da kayayyakin jinya 30 da ke sahun gaba a duniya.

A cikin shekaru uku da suka wuce, tashar Hainan ta kuma kaddamar da jerin matakai na saukaka harkokin shiga kasuwa. A nan tashar, fannoni kalilan ne aka haramta ’yan kasuwar ketare su zuba jari, baya ga haka, an kuma tsara manufar haraji mai gatanci kan kudin shigar da ake samu don karfafa gwiwar kamfanoni da kuma kwararru, manufofin da suka sa ingantattun kamfanoni masu jarin waje sun yi ta zuba jari a tashar. Xu Yao, manajan kamfanin Tesla reshen yankin Hainan ya ce, za su habaka aikin gina tsarin yi wa motoci caji. Yana mai cewa,Tesla nau’in mota ce dake aiki da sabbin makamashi, za mu inganta gina tsarin yi wa nau’in motoci caji. Gaba daya za mu shimfida tsari a sassan tsakiya da gabashi da kuma yammacin tsibirin.”

Tashar ciniki marar shinge ta Hainan ta cika shekaru uku da kafuwa_fororder_968

Tun bayan da aka fara aiwatar da sabuwar manufar haraji kan kayayyakin da ake shigowa kasar a Hainan, karin masu sayayya na zuwa wurin domin sayen kayayyaki. A wata mai zuwa kuma, kasar Sin za ta gudanar da bikin baje kolin kayayyakin masarufi na kasa da kasa karo na farko a Hainan, inda za a baje kolin kayayyaki masu sanannun tamburan kasa da kasa kusan 1200, wadanda za su dau kimanin kashi 80% na fadin bikin. Ana ganin cewa, hakan ya faru ne a sakamakon babbar kasuwar kasar Sin da ma yadda kamfanonin kasa da kasa suke da imanin karfafa hadin gwiwarsu da kasar Sin ta fannonin zuba hari da ciniki. Bernardino Regazzoni, jakadan kasar Switzerland a kasar Sin ya ce, “Bikin baje kolin da za a gudanar wani muhimmin al’amari ne ga kasar Sin da Hainan da ma kamfanonin kasa da kasa, wanda kuma yake alamta wani karin ci gaban da aka samu a tashar ciniki maras shinge ta Hainan, da ma yadda kasar Sin ke gaggauta dunkulewa da tattalin arzikin duniya.” (Lubabatu)