logo

HAUSA

Rahoto: Ciniki ta intanet ya bunkasa kasuwancin yankunan karkarar Sin

2021-05-06 10:23:32 CRI

Rahoto: Ciniki ta intanet ya bunkasa kasuwancin yankunan karkarar Sin_fororder_210506-cinikayya ta intanet

Wani rahoto ya nuna cewa, cinikayya ta intanet ya sauya tsarin kasuwancin kayayyaki da ayyukan hidima a yankunan karkarar kasar Sin.

Alkaluma sun nuna cewa, a halin yanzu, mazauna karkara sun fi mayar da hankali wajen sayen kayayyakin amfanin gida da na’urorin zamani ta hanyar intanet, majalisar bunkasa kasuwancin kasa da kasa ta kasar Sin ta bayyana hakan cikin rahotonta.

Rahoton ya ce, mazauna karkara sun fadada hanyoyin cinikayyar amfanin gonarsu ta hanyar intanet kuma hakan ya taimaka musu wajen samun karin kudade, kana lamarin ya haifar da saurin bunkasuwar harkokin kasuwanci a yankunan karkara.

Tsakanin watannin Janairu zuwa Maris, cinikayyar intanet ta mazauna karkara ya kai Yuan biliyan 439.79, kwatankwacin dala biliyan 68, inda ya karu da kashi 35.3 bisa 100 idan an kwatanta da makamancin lokacin shekarar bara, kamar yadda alkaluman ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta bayyana.

A cewar ma’aikatar, cinikayyar kayayyakin amfanin gona ta intanet ya kai Yuan biliyan 105.58 a makamancin lokacin, inda ya karu da kashi 4.9 bisa 100 a makamancin lokacin bara. (Ahmad)