logo

HAUSA

Cibiyar nazarin Birtaniya: Sin za ta samu gagarumar bunkasuwar cinikin waje a ragowar watannin shekarar 2021

2021-04-14 10:49:04 CRI

Cibiyar nazarin Birtaniya: Sin za ta samu gagarumar bunkasuwar cinikin waje a ragowar watannin shekarar 2021_fororder_210414-cinikin wajen Sin

Rahoton da cibiyar kwararrun masana tattalin arziki ta Oxford ta kasar Birtaniya ta bayyana cewa, ana sa ran hada hadar shigi da fici na kasar Sin zai samu matukar bunkasuwa a raguwar watannin shekarar nan ta 2021 yayin da ake samun farfadowar tattalin arziki na cikin gida da na kasa da kasa.

A cewar rahoton, ana sa ran hajojin da ake fitarwa zuwa ketare zai cigaba da karuwa a rubu’i na biyu, kana karfin farfadowar tattalin arzikin duniya zai karawa hada hadar fitar da kayayyakin kasar Sin zuwa ketare matukar bunkasuwa a cikin shekarar ta 2021, duk kuwa da yiwuwar samun raguwar bukatun da ake da shi masu alaka da annobar CPVID-19 a wannan shekarar.

A cewar rahoton cibiyar nazarin tattalin arzikin, samun jinkiri a fannin fiton kayayyaki ta ruwa na duniya zai iya rage hasashen karuwar alkaluman fitar da kayayyaki zuwa ketare, sai dai rawar da kasar Sin ke takawa a fannin samar da kayayyaki a kasuwannin duniya ba lallai ne ya ragu ba.

Rahoton ya bayyana cewa, sabanin yadda ake tsammani, hada hadar fitar da hajojin Sin zuwa ketare ya samu karbuwa a kasuwannin duniya tun bayan barkewar annobar, kuma ana kara samun ingantuwar bukatun nau’ikan kayayyaki daban daban a watannin da suka gabata.

Wannan rahoto na zuwa ne bayan wasu alkaluma da hukumomin kasar Sin suka fitar tun da farko dake nuna cewa hada hadar fici da shigin kayayyaki na kasar ya karu da kashi 29.2 bisa 100 idan an kwatanta da na makamancin lokacin bara wanda ya kai yuan triliyan 8.47 kwatankwacin dala triliyan 1.29 a rubu’in farko na shekarar 2021. (Ahmad Fagam)