logo

HAUSA

Xi Jinping ya taya shugaban Burkina Faso murnar ci gaba da mulkinsa

2020-12-08 11:10:41 CRI

Jiya Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika sako ga takwaransa na kasar Burkina Faso Christian Kaboré, domin taya masa murnar lashen zaben yin zarce.

A cikin sakonsa, Xi ya nuna cewa, kasashen biyu sun kara amincewa da juna a siyasance da habaka hadin gwiwarsu a fannoni daban daban a shekarun baya-bayan nan, kuma suna bullo da makoma mai haske tsakaninsu. A cewarsa, yana dora babban muhimmanci kan bunkasuwar dangantakar kasashen biyu da kuma zumuncin dake tsakaninsu, yana fatan kara yin kokari tare da shugaba Christian Kaboré don ingiza dangantakar kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi, da nufin amfanawa jama’ar kasashen biyu. (Amina Xu)