logo

HAUSA

Amurka ba ta mai da hankali kan bincike da aka yi don gano asalin cutar COVID-19

2021-06-02 16:02:38 CRI

Amurka ba ta mai da hankali kan bincike da aka yi don gano asalin cutar COVID-19_fororder_微信图片_20210602160214

By CRI Hausa

Kwanan baya, wasu ’yan siyasar Amurka sun dora laifi kan kasar Sin, game da bincike da ake yi na gano asalin cutar COVID-19, har ma gwamnatin kasar ta umurci hukumar leken asirin ta, da ta jagoranci wannan aiki. Sai dai kuma kasashen duniya sun nuna matukar rashin jin dadi game da hakan.

Kowa ya san cewa, binciken asalin cutar aikin kimiyya ne, kuma hanya daya tilo da za a bi shi ne, amfani da kimiyya a maimako dogaro da hukumar leke asiri wadda ta taba kirkiro dimbin munanan laifuka. Wasu ’yan siyasan Amurka suna son dora laifi kan kasar Sin, domin boye laifuffuka nasu na kasa daukar matakai masu dacewa na yakar annobar a cikin kasar Amurka, da ma yunkurin hana bunkasuwar kasar Sin. Matakin da ke keta hurumin kimiyya, da yin biris da rayukan Bil Adama, ya kasance kamar wani wasan siyasa mai ban dariya. Ko shakka babu, hakan zai jefa lafiyar al’ummun duniya cikin mawuyacin hali mai tsanani.

Abin da aka sa gaba wajen samun sakamako mai dacewa game da wannan bincike shi ne, goyon bayan jagorancin WHO, da kuma tsayawa masanan kiwon lafiya, ta yadda za su gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

A sa’i daya kuma, kasancewar an gano mutane masu harbuwa da cutar na matakin farko a wurare da dama a duniya, ya nuna cewa, ya kamta a gudanar da irin wannan bincike a kasashe daban-daban cikin adalci.

Binciken asalin cutar aikin kimiyya ne, ba wasa na dora laifi kan wasu ba, balle ya zama hujja da wasu ’yan siyasar Amurka za su yi amfani da ita wajen cimma buri su. Hausawa kan ce, “Munafurcin dodo ya kan ci mai shi”. (Amina Xu)