logo

HAUSA

Manyan jami’an Sin da Amurka sun zanta game da dangantakar tattalin arzikin kasashen biyu

2021-06-02 10:19:26 CRI

Manyan jami’an Sin da Amurka sun zanta game da dangantakar tattalin arzikin kasashen biyu_fororder_210602-Liu He

Mataimakin firaministan Sin, kana jagoran tawagar Sin dake tattaunawa da tsagin Amurka game da cikakkun batutuwan dake shafar tattalin arziki Liu He, ya zanta ta kafar bidiyo da sakataren baitulmalin Amurka Janet Yellen.

Yayin tattaunawar ta safiyar yau Laraba, jami’an biyu sun amince da muhimmancin karfafa dangantakar tattalin arziki dake gudana tsakanin Sin da Amurka. Sun kuma amince da ci gaba da yin musaya a fannonin da suka jibanci raya tattalin arziki, da hadin gwiwa, da cudanyar sassa daban daban, bisa tushen daidaito da martaba juna.

Kaza lika jami’an sun yi musayar ra’ayoyi kan batutuwan da suke mayar da hankali a kai, tare da shan alwashin ci gaba da tuntubar juna yadda ya kamata. (Saminu Hassan)