logo

HAUSA

Kasar Sin tana kokarin taimakawa kasashen Afirka dakile annobar COVID-19 da farfado da tattalin arziki

2021-05-23 21:07:37 CRI

Kasar Sin tana kokarin taimakawa kasashen Afirka dakile annobar COVID-19 da farfado da tattalin arziki_fororder_20210523-sharhi-Afirka-Bello

Kasar Sin a kwanakin baya ta bayyana wasu shawarwari da alkawurra masu muhimmanci, na taimakawa kasashe masu tasowa, musamman ma kasashen Afirka, wajen dakile cutar COVID-19, da farfado da tattalin arzikinsu.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron shugabannin kasashe daban daban dangane da batun kiwon lafiya, a Juma’a 21 ga wata, inda ya ce kasar Sin tana goyon bayan ra’ayin soke ikon mallakar ilimi game da alluran rigakafin cutar COVID-19, gami da fatan ganin kamfanonin kasar sun yin hadin gwiwa tare da kasashe masu tasowa, wajen samar da rigakafin.

Kafin haka kuma, a ranar 19 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya jagoranci taron kwamitin sulhu kan zaman lafiya da tsaro a kasashen Afirka, bisa matsayinsa na shugaban kwamitin sulhu na MDD na karba-karba.

A nasa bangare, mataimakin firaministan kasar Sin Han Zheng, ya halarci taron gidauniyar tara kudade don raya nahiyar Afirka, a ranar 18 ga wata, inda ya gabatar da shawarwarin rage yawan bashin da ake bin kasashen Afirka, da kara zuba jari a kasuwannin nahiyar cikin dogon lokaci, da taimakawa kasashen Afirka samun ci gaba, tare da kare muhalli.

Wadannan shawarwari da alkawurra sun nuna yadda kasar Sin take kokarin biyan bukatun kasashen Afirka na shawo kan annobar COVID-19, gami da farfadowar tattalin arziki. Kana kafin hakan, kasar Sin na ta kokarin daukar takamaiman matakai don taimakawa dakile cutar COVID-19 a kasashen Afirka. Ya zuwa karshen watan Maris na bana, kasar Sin ta yi jigilar kayayyakin kandagarkin cuta har sau 120 zuwa nahiyar Afirka, da tura tawagogin kwararrun likitoci zuwa kasashe 15 dake nahiyar, gami da samar da alluran rigakafin cutar COVID-19 ga wasu kasashe 35 dake Afirka, da kungiyar kasashen Afirka AU.

A farkon wannan watan da muke ciki, kasar Masar ta ce za ta fara samar da alluran rigakafin cutar COVID-19 na kamfanin SINOVAC na kasar Sin a watan Yuni mai zuwa, ta yadda za ta zama kasar farko dake nahiyar Afirka wadda ta iya samar da alluran rigakafin. An ce ta haka za a saukaka ayyukan jigilar da ajiye alluran, da taimakawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar Masar da na sauran kasashen dake nahiyar Afirka.

Abun da za mu iya tabbatar da shi shi ne, ko a lokacin da ake fama da cutar COVID-19, ko bayan an samu kawar da annobar baki daya, kasar Sin za ta taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa kasashen Afirka farfado da tattalin arziki.

Da farko, shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” da kasar Sin ta gabatar za ta taimaka wajen karfafa hadin kan kasashen Afirka da kasar Sin a fannin tattalin arziki.

Ko da yake annobar COVID-19 ta haifar da tsaiko ga wasu bangarorin tattalin arzikin kasashe daban daban, amma tsarin shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” ta sa masana’antun kasashe daban daban na ci gaba da gudana. A shekarar 2020, yawan kayayyain da aka yi jigilarsu bisa layukan da suka hada kasar Sin da sauran kasashen mambobin shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” ya karu da kaso 104.9. Kana an bude karin wasu layukan zirga-zirga, ciki har da layin da ya hada garin Nanchong dake kudu maso yammacin kasar Sin da kasar Najeriya. Ban da wannan kuma, annobar COVID-19 ba ta hana kamfanonin gini na kasar Sin gudanar da ayyukan gina kayayyakin more rayuwar jama’a a kasashen Afirka ba, inda yawancin ayyukansu na gudana yadda ake bukata.

Na biyu, fasahohin zamani na baiwa Sin da Afirka karin damammakin hadin gwiwa.

Sakamakon yadda annobar COVID-19 ta hana mutane zirga-zirga, wasu fasahohi na zamani na samun ci gaba cikin sauri, musamman ma fasahar sadarwa ta 5G, da ta sayen kaya ta hanyar shafin yanar gizo ta Internet, da fasahar koyon ilimi daga gida, da dai sauransu.

Wannan ci gaba yana haifar da alfanu ga kasashen Afirka gami da kasar Sin. Inda ake iya ganin bangarorin sadarwa, da ciniki ta kafar Internet na bunkasuwa cikin sauri a kasashen Afirka. Kana kasar Sin a nata bangaren, tana kokarin gina kayayyakin more rayuwa masu alaka da fasahohin zamani a nahiyar Afirka, tare da raba wa kasashen Afirka fasahohinta a fannonin ciniki ta kafar Internet, da jigilar kayayyaki, da dai sauransu.

Na 3, kasashen Afirka da kasar Sin za su iya hadin gwiwa da juna a kokarin raya masana’antu mai alaka da aikin kare muhalli.

Yaduwar annobar COVID-19 ta sa dan Adam tunanin tasirin zaman rayuwarsu kan muhallin halittu. Tuni kasar Sin ta samar da manufar kare muhalli tare da samun moriya daga wani ni’imtaccen muhalli, wadda ta kunshi fasahohin da sauran kasashe masu tasowa za su iya koya. Yayin da kasashen Afirka a nasu bangaren, su ma suna kokarin karkata ga makamashin da basu gurbata muhalli, da rage hayaki mai sa dumamar yanayi da suke fitarwa. Kasar Sin ta dade tana kokarin hadin gwiwa da kasashen Afirka a kokarinsu na samun ci gaban kasa mai dorewa. Nan gaba za su iya karfafa hadin gwiwarsu a fannonin tsara manufofi, da mika fasahohi, da gina kayayyakin more rayuwa da ake yin amfani da su wajen kare muhalli, da dai makamantansu.

Ko da yake annobar COVID-19 ta hana mutane zirga-zirga cikin ‘yanci, amma ba za ta hana hadin gwiwar kasashen Afirka da kasar Sin ba. Bisa tushen hadin gwiwarsu irin ta morewa juna, da suka taba gudanar da su a baya, Sin da Afirka za su yi kokarin dakile cutar COVID-19, da farfado da tattalin arzikinsu tare, gami da kafa wata al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya tsakaninsu. (Bello Wang)

Bello