logo

HAUSA

Kura ta tirnike filin jirgin saman Goma a jamhuriyar Kongo sakamakon aman wutan dutse

2021-05-23 15:54:28 CRI

Kura ta tirnike filin jirgin saman Goma a jamhuriyar Kongo sakamakon aman wutan dutse_fororder_congo

Rahotanni daga jamhuriyar demokaradiyyar Kongo sun bayyana cewa, kura ta tirnike filin jirgin sama birnin Goma dake gabashin kasar, bayan aman wutan dutsen da ya faru a ranar Lahadin nan daga wani babban tsaunin Nyiragongo, hukumomin kasar sun bayyana aniyarsu na kwashe mazauna yankin.

A cewar kakakin gwamnatin kasar Patrick Muyaya, gwamnati ta shirya aikin kwashe mazauna yankin.

A sakon da ya wallafa a shafin twita, Muyaya ya ce, gwamnati tana tattaunawa game da daukar matakan gaggawa kan faruwar lamarin.

Dubban mazauna birnin Goma sun tsere daga birnin da kafarsu zuwa garin dake makwabtaka da kasar Rwanda, yayin da birnin mai yawan al’umma kusan miliyan 2 suke fama da kurar aman wutar dutsen da ta tirnike inda ta mayar da yankin launin ruwan dorawa.

Shugaban kasar DRC, Felix Tshisekedi, yana kan hanyarsa ta komawa kasar daga Turai domin sanya ido wajen tafiyar da ayyukan agaji da kula da yanayin rayuwar al’ummar lardin Kivu dake gabashin kasar, kamar yadda fadar shugaban kasar ta ayyana.(Ahmad)

Ahmad