logo

HAUSA

Wang Yi ya halarci liyafar ranar Afirka da aka shirya a Beijing

2021-05-26 13:00:17 CRI

Jiya ne dan majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya halarci liyafar ranar Afirka da aka shirya a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda ya bayyana bukatar Sin da Afirka su yi aiki tare, don samar da wani sabon yanayi a hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu.

A madadin gwamnatin kasar Sin, Wang Yi ya mika gaisuwa ga jakadun kasashen Afirka dake kasar Sin, da kasashen Afirka da ma al’ummominsu. Yana mai cewa, ranar Afirka, rana ce mai muhimmanci ga al’ummun Afirka, a gwagwarmayar da suka yi ta neman ‘yanci da karfafa hadin kai.

Ya kuma jaddada cewa, kasar Sin ta taya kasashen Afirka murnar ranar Afirka sakamakon kyakkyawar huldar da ke tsakanin bangarorin biyu. Batun karfafa hadin kai tsakanin Sin da kasashen Afirka, na daga cikin abu mafi muhimmanci, da Sin take karfafawa a manufofinta na diflomasiya. Minista Wang ya ce, Sin da Afirka suna yaki kafada da kafada a gwagwarmayar neman ‘yanci da kare muradun kasashensu, a hannu guda kuma, suna goyon bayan juya kan batutuwan dake shafar babbar moriyarsu.

Wang Yi, ya kuma gabatar da wasu shawarwari guda hudu, kan yadda za a samar da sabon yanayi a hadin gwiwar sassan biyu. Ya yi kira ga bangarorin biyu, da su yi kokarin ganin an samu nasarar taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) dake tafe, su kuma yi aiki tare, don ganin bayan annobar COVID-19 cikin hanzari, da yayata yadda za a raya hadin gwiwa yadda ya kamata, da kuma karfafa hadin gwiwa a harkokin kasa da kasa. (Ibrahim)