logo

HAUSA

Xi Jinping ya jagoranci taron karawa juna sani game da bibiyar gagarumin aikin sauya akalar ruwa da ake yi a lardin Henan

2021-05-14 21:00:46 CRI

Xi Jinping ya jagoranci taron karawa juna sani game da bibiyar gagarumin aikin sauya akalar ruwa da ake yi a lardin Henan_fororder_微信图片_20210514210236

A yau Juma’a ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jagoranci taron karawa juna sani, game da aiwatar da matakan cimma nasarar bibiyar gagarumin aikin nan, na sauya akalar ruwa da ake yi a lardin Henan.

Yayin taron, Xi Jinping, ya jaddada bukatar sake duba na tsanaki, game da sabon yanayin da ake ciki, dangane da aikin sauya alakar ruwa daga kudu zuwa arewa, tare da karfafa aiwatar da tsarin kimiyya, da aiwatar da wannan muhimmin aiki, domin habaka amfani da albarkatun ruwa ta hanyoyi mafiya dacewa. (Saminu)