logo

HAUSA

Sin ta bukaci Amurka ta daina yin hulda a hukumance da yankin Taiwan

2020-11-12 11:04:36 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya ce, gwamnatin kasar ta bukaci Amurka da ta dakatar da dukkan huldodi da yin mu’amala a hukumance da yankin Taiwan.

Wang Wenbin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, ya bayyana hakan a taron manema labarai yayin da aka nemi ya yi tsokaci game da batun tattaunawar tattalin arziki da aka shirya gudanarwa tsakanin kasar Amurka da yankin Taiwan.

Wang ya ce, “Mun bukaci Amurka da ta mutunta “manufar kasar Sin daya tak a duniya” da yarjejeniyoyin hadin gwiwa uku tsakanin Sin da Amurka".

Ya kamata Amurka ta yi kaffa-kaffa da yin taka tsan-tsan game da batutuwan dake shafar yankin Taiwan kuma bai kamata ta aike da munanan sakonni ga ‘yan a-ware masu neman ‘yancin kan Taiwan ba, domin kaucewa haifar da mummunanr illa kan dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka da dorewar zaman lafiya da kwanciya hankali a gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan, inji kakakin.

Wang ya kara da cewa, babu wani yunkuri da zai taba yin nasara kan duk wani zagon kasa dake neman lalata dangantakar dake tsakanin babban yankin kasar Sin da yankin Taiwan.

Ahmad Fagam