logo

HAUSA

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta soke ziyarar da jakadiyarta a MDD za ta yi a Taiwan

2021-01-13 14:50:58 CRI

Bias labarin da kamfanin dillancin labaru na Reuters ya bayar, an ce, a ranar 12 ga wata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka ya sanar da cewa, ma’aikatar ta soke dukkan ziyarce-ziyarce da za a yi a kashen ketare a wannan mako, ciki had da ziyarar da jakadiyarta a MDD madam Kelly Craft za ta yi a Taiwan.

A cewar kamfanin dillancin labaru na Reuters, ga alama ziyarar madam Kelly Craft a Taiwan, wani kokari ne na daban, da gwamnatin Donald Trump ta yi don nuna tsattauran ra'ayi ga kasar Sin, kafin a rantsar da Joseph Biden a matsayin shugaban Amurka. Tuni kuma kasar Sin ta bayyana adawar ta da wannan ziyara.  (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan