logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Amurka Ke Kara Rura Zaman Tankiya A Zirin Gaza

2021-05-18 20:25:22 CRI

Kasar Sin ta yi Allah wadai, da yadda Amurka ke kara rura wutar tashin hankali tsakanin Isra’ila da Palasdinu, bayan da ta kawo cikas ga sanarwar hadin gwiwar kwamitin sulhun MDD, da ke kira a gagguta tsagaita bude wuta a karo na uku.

A ranar Lahadin da ta gabata ne, kwamitin sulhun ya kira wani taron gaggawa, inda kasashen Sin da Norway, da Tunisiya suka jagoranta, don tattauna yanayin da ake ciki a zirin Gaza. Sai dai kuma, saboda adawar da Amurka ta nuna, an kammala taron ba tare da cimma wani sakamako ba.

Da yake magana kan wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Zhao Lijian, ya bayyana rashin jin dadin kasarsa da ma kasashen duniya, kan yadda Amurka ta kawo cikas ga sanarwar hadin gwiwar, yana mai cewa, Amurka tana adawa da nuna adalci.

A cewar Zhao, galibin kasashe mambobin kwamitin sulhun, suna kira da a hanzarta tsagaita bude wuta, don kaucewa tsanantan yanayi da asarar rayuka. A halin da ake ciki, Amurka, maimakon ta sa kaimi wajen ganin an tsagaita bude wuta, sai ta zabi kara rura tashin hankali, ta hanyar dakile kokarin kasa da kasa.

Rahotanni na nuna cewa, a karkashin gwamnatin Biden, Amurka ta amince ta sayarwa Isra’ila makamai da darajarsu ta kai dalar Amurka miliyan 735.

Ibrahim